Adadin bashin da ake bin Nijeriya na shekarar 2022, ya kai Naira tiriliyan 46.25 ko kuma dala biliyan 103.11, a cewar wani sabon alkaluman da ofishin kula da basussuka (DMO) ya fitar ranar Alhamis.
Sabon alkaluman ya kunshi jimillar basussukan cikin gida da waje na gwamnatin tarayya da na kananan hukumomi (gwamnonin jihohi 36 da babban birnin tarayya).
- Dakarun Soji  4 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Bauchi
- NDLEA Ta Cafke Wata Matar Aure Tana Sayar Da Tabar Wiwi Lokacin Azumi A Katsina
Dangane da kididdigar, jimillar bashin cikin gida ya kai Naira tiriliyan 27.55, kwatankwacin dala biliyan 61.42, yayin da jimillar bashin waje ya kai Naira tiriliyan 18.70 kwatankwacin dala biliyan 41.69.
Ofishin basussukan ya bayar da dalilan da ya sa aka samu karuwar basukan da ake bin gwamnati, wanda ya hada da sabbin rancen da gwamnatocin tarayya da na kananan hukumomi ke yi, musamman don samar da gibin kasafin kudi da aiwatar da ayyuka.
Bayar da takardun shaida da gwamnatin tarayya ta yi don daidaita wasu lamura, shi ma ya taimaka wajen bunkasa hannayen jarin.
Yunkurin da gwamnati ke ci gaba da yi na kara samun kudaden shiga daga albarkatun mai da wadanda ba na mai ba ta hanyar tsare-tsare irin su Dokar Kudi da dabarun tattara kudaden shiga, ana sa ran za su tallafa wa dorewar bashi.
A halin da ake ciki kason cikin gida (GDP) na ranar 31 ga watan Disamba, 2022, ya kai kashi 23.20 cikin 100 kuma ya nuna an samu karuwa kadan daga adadi na 31 ga watan Disamba, 2022, da kashi 22.47 bisa dari.
Adadin kashi 23.20 cikin 100 yana cikin kayyade kashi 40 cikin 100 da Nijeriya ta gindaya wa kanta, yayin da kashi 55 cikin 100 na Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya, da kuma kayyade bashi ke da kasha 70 cikin 100 da Kungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta bayar.