Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce fannin wutan lantarkin Nijeriya na fuskantar barazana ta wanzuwa sakamakon bashin naira tiriliyan 4 da kamfanonin samar da wutar lantarki (GENCOs) ke bi, nauyin da aka tara tun shekarar 2015 wanda ke ci gaba da gurgunta ingancin samar da wuta da kashe ƙwarin gwiwar masu zuba jari.
Adelabu, wanda ya yi wannan gargaɗin yayin zaman ganawa da shugaban ƙungiyar kamfanonin samar da wutar lantarki (APGC) da ya gudana a fadar shugaban ƙasa, ya ce, muddin ba a samar da tallafin gaggawa ba, ɓangaren na fuskantar daukewa, lamarin da ke ƙara dagula lamarin tattalin arziki da kuma tsadar kayayyaki.
Ya yi kira da a samar da biyan wani kaso na basukan cikin gaggawa, ya ce, gwamantin tarayya ta bijiro da tsare-tsaren da za su taimaka wajen bai wa ɓangaren wutar lantarki damar tsayuwa da ƙararsa a ɓangaren kasuwanci.
- Bankuna Sun Karbi Bashin Naira Tiriliyan 3 Daga CBN Cikin Mako 3
- Kamfanonin Lantarki Na Shirin Shiga Yajin Aiki Kan Bashin Naira Tiriliyan 4
Ya jaddada da roƙon shugaban ƙasa na GENCOs da cibiyoyin kuɗi don su ƙara haƙuri yayin da gwamnati take kan kammala aikin tantance.
Ya fahimci takaicin masu saka hannun jari, amma ya jaddada buƙatar tabbatar da cewa duk wani abin da ake da’awa a kansa to akwai buƙatar bincike da tabbatarwa.
A cewar Adelabu, har yanzu dai wutar lantarki ne ƙashin bayan kamfanoni a Nijeriya da kuma tattalin arziki, ya nemi haɗin kan dukkanin wadanda lamarin ya shafa domin sake farfaɗo da sashin wutar lantarki yadda ya kamata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp