Nijeriya ta kashe jimillar kudade har Naira tiriliyan 13.12 wajen biyan basuka a shekarar 2024, wanda ke nuni da kaso 68 cikin 100 na kari da aka samu daga naira tiriliyan 7.8 a shekarar 2023, a cewar sabon rahoton da Ofishin kula da basuka (DMO) ya fitar.
Bayanai sun lura cewa kudaden biyan basussukan da aka yi a shekarar 2024 ya zarce kasafin da aka ware na naira tiriliyan 12.3 na shekarar.
- Sin Ba Za Ta Razana Da Zuwan Yakin Cinikayya Ba
- Huawei Ya Daddale Yarjejeniya Da Kenya Don Habaka Kwarewar Ma’aikatan Kasar A Fannin Dijital
Kudaden da ake kashewa fiye da yadda ake tsammani na nuna karuwar matsi na wajibcin ciwo bashi a kan dorewar kasafin kudin kasar nan.
A cikin kasafin 2025, gwamantin tarayya ta ware naira tiriliyan 16 domin biyan basuka, hakan da ke nuni da irin yadda gwamnatin ta sanya himma wajen kula da lamuran basuka.
Wannnan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna fargaba kan yawan ciwo basuka da kuma karin nauyin da suke tattare da ciwo basuka, lamarin da ke kara sanya damuwowi ga kasafin kasar.
Kudin biyan bashin cikin gida na shekarar 2024 ya kai naira tiriliyan 5.97, wanda hakan ke nuna karin kashi 14.15 cikin 100 daga naira tiriliyan 5.23 da aka samu a shekarar 2023. Karuwar ana danganta shi da karuwar kudin ruwa da karin lamuni na cikin gida.
Nijeriya dai ta kashe dala biliyan 4.66 (kwatankwacin naira tiriliyan 7.15 kan farashin canjin naira 1,535.32/$1), wanda hakan ya nuna karuwar kashi 167 cikin 100 daga naira tiriliyan 2.57 da aka samu a shekarar 2023.
Yawan kudin biyan basussuka na waje yana da nasaba da hauhawar farashin ruwa a duniya da kuma faduwar darajar naira, lamarin da ya sa bashin dala ya yi tsada wajen aiki.
Duk da yawan kudin basukan da ke kan Nijeriya, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ciwo basuka kadan ta yi amfani da su cikin hanyoyin da suka dace.
Shettima ya bayyana haka ne a karshen makon da ya gabata a Abuja, yayin wani taron da kungiyar akanta ta kasa ta kasa da kuma cibiyar harajin ta Nijeriya ta shirya.
Mataimakin shugaban kasar, wanda ya samu wakilcin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, Dakta Tope Fasua, ya bayyana cewa sannu a hankali ana sake fasalin tsarin karbar basussukan da gwamnati ke yi domin rage bashin.
Ya kuma bayyana cewa, duk da rancen da aka karbo a baya-bayan nan da ya jawo cece-kuce, yanzu Nijeriya na kan hanyar karbar rancen kadan tare da kokarin rage gibin kasafin kudaden da ake fuskanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp