A ranar Litinin, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ci tarar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abduljabbar Kabara da ke tsare, tarar Naira miliyan 10, bisa laifin shigar da kara kan tauye masa hakkinsa wanda kotun tace karar “cin zarafin kotu ne.”
Mai shari’a Emeka Nwite, a hukuncin da ya yanke, ya bayar da umarnin a biya wadanda ake karan kudaden; Babbar Kotun Sharia ta Kofar Kudu da gwamnatin jihar Kano.
Mai shari’a Nwite ya kuma bukaci lauyan Kabara, Shehu Dalhatu da ya biya gwamnatin jihar Naira 100,000.
Nwite ya ce da zarar kotu ta gamsu cewa karar da aka shigar cin zarafi ne na wata shari’a, to kotu na da hakkin hukunta wanda ya shigar da karar.
Ya ce matakin da lauyan Kabara ya dauka na da nufin samun sassauci ko samun nasara ta kowane Irin hali.
Nwite ya ce shigar da kara a cikin wata kara mai lamba: FHC/KN/CS/185/2022 a Kano da kuma zuwa Abuja don shigar da wata mai lamba: FHC/ABJ/CS/1201/2022 kan batu daya kuma lauya daya, ya sabawa Dokar kotu.