Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce, Majalisar dokokin jihar Adamawa, zata ayyana mamba mai wakiltar karamar hukumar Hong a Majalisar, Honarabul Batiya Wesley, a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin jihar na 8.
Wata majiya daga majalisar ta shaidawa LEADERSHIP Hausa hakan a ranar Litinin 12, ga watan Yunin 2023.
“Abin da ya rage shi ne ‘Yan majalisar su tabbatar da zabin da suka yi wa Honarabul Batiya Wesley a zauren majalisa, ranar Talata” Cewar majiyar.
Karin bayani zai zo daga baya.