Gwamnatin Jihar Bauchi ta datse tare da kawo karshen aikin wani ma’aikacin gwamnati mai suna Ibrahim Garba da ke da matsayin babban mataimakin sakatare (CSA) bisa samunsa da laifin badakalarr kudade.
Ma’aikacin da aka kora ya na aiki ne da hukumar kula da fansho ta jihar an samesa ne da laifin handama da babakeren naira miliyan N3, 017, 919.30 mallakin wani dan fanshi da ya rigamu gidan gaskiya mai suna Audu Mohammed.
A cewar sanarwar da jami’in watsa labarai na hukumar kula da ma’aikata ta jihar Bauchi (BSCSC), Malam Saleh Umar ya fitar a ranar Talata na cewa, “Ibrahim Garba dai, kwamitin ladabtarwa na hukumar fansho ya sameshi hannu dumu-dumu da yin wasu ‘yan dabarbaru wajen sauya asusun ajiyar bankin Abdu Mohammed wanda ya rigamu gidan gaskiya (Mamaci) da asusun ajiyarsa da hakan ya ba shi damar canza maballen sirri bayan da ahlin mamacin suka kai masa rahoton rasuwar Malam ‘Abdu’”.
Saleh Umar ya kara da cewa, hukumar ta amince da kawo karshen aikin Ibrahim Garba ne a yayin zamanta karo na 17 da aka gudanar a ranar 1 ga watan Agustan 2023.
Umar ya kara da cewa, “An samu jami’in da mummunar da’a ta hanyar shigar da kansa cikin badakalar albashi/fansho. Matakin nasa ya saba balo-balo wa tanade-tanaden dokokin aikin gwamnati (PSR) 0327(XI) da ta shafi almubazzarancin kudade.”
Sanarwar ta kara da cewa, “Ibrahim Garba ya amshi haramtaccen kudin fansho na watanni hamsin da biyar (55) da ya kai naira N54,871.26 kowace wata na tsawon shekaru hudu da watanni bakwai, sannan, adadin kudin da ya hamdame sun kai naira miliyan N3,017,919.30, kuma, kai tsaye za a kwatosu daga cikin hakkokinsa.”
Umar ya kuma nakalto shugaban hukumar kula da ma’aikata na jihar Bauchi, Alhaji Abubakar Usman Madakin Bunun Bauchi, da ya jagoranci zaman da aka gudanar wajen daukan wannan matakin, ya gargadi da jan kunnen ma’aikatan jihar da su kasance masu jin tsoron Allah da gudanar da aikinsu bisa da’a da bin dokoki da ka’idoji domin kauce wa shiga irin wannan matakin.
Shugaban ya ce, dole ne ma’aikata su kasance masu bin dokoki da ka’idojin aikin gwamnati domin tsarkakewa da tsaftace sashin aiki a kowani lokaci, ya na mai gargadin cewa duk wani ko wasu da aka kama da irin wannan ko makamancin wannan laifin tabbas zai fuskanci fushin hukumar ba makawa.
Ya bada tabbacin cewa, hukumar ba za ta zura ido tana kallo ko ta bari wasu bata-garin ma’aikata su kawo cikas ko bata kokarin gwamnati na kawo cigaba ga jihar musamman ta fuskacin kula da walwala da jin dadin aiki, sashin albashi da kuma biyan fansho.