Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya amince da haramcin yin hawan Sallah da rundunar ‘yansandan jihar Kano ta yi a kwanakin baya, inda ya ce matakin ya zama wajibi domin dorewar zaman lafiya da ci gaban jihar.
Saboda haka, Sarki Sanusi II ya bayyana cewa bikin gargajiya na shekara-shekara da aka saba gudanarwa a karshen watan Ramadan ba lamari ne na “ko a mutu ko a yi rai ba, illa kawai alamar al’ada ce tun karni na 15”.
- Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Fiji: Ya Kamata A Koyi Fasahohin Da Kasar Sin Ta Samu A Fannin Raya Kasa
- Tawagar Ma’aikatan Ceto Ta Kasar Sin Ta Isa Birnin Yangon Na Kasar Myanmar
Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin manyan malaman addinin Musulunci da kuma manyan mutane wajen buda baki a fadarsa da yammacin ranar Asabar.
Sarkin Kano mai daraja ta daya wanda ya bayyana zaman lafiya a matsayin kashin bayan ci gaban kowace al’umma, don haka, ya amince da janye duk wasu shirye-shiryen bikin hawan Sallah mai ban sha’awa, wanda ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da al’adu (UNESCO) ta bayyana a matsayin gadon bil’adama mara misaltuwa.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Adamu Bakori ne ya sanar da dakatar da bikin hawan Sallah, saboda barazanar tsaro da jami’an leken asiri suka rahoto a jihar.
Dangane da haka, Sarki Sanusi ya yi kira ga al’umma da su kasance masu zaman lafiya da bin doka da oda tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda a lokutan bukukuwan Sallah da kuma bayan bikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp