• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bayan Kin Gaskiya…

by CMG Hausa
2 years ago
South Korean fishermen stage a rally against the planned release of treated radioactive water from the wrecked Fukushima nuclear power plant, in front of the National Assembly in Seoul, South Korea, Monday, June 12, 2023. (AP Photo/Ahn Young-joon)

Da alamun dai Japan ba ta hakura da shirinta na zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku ba, duk da kiraye-kiraye da sassan kasa da kasa ke mata kan illar da hakan ga rayuwar daukacin bil-Adama.

Wannan ne ma ya sa kasar Sin ta sake ankarar da Japan din, da ta yi la’akari da kimiya, ta kaucewa aukuwar hadari da ma yin komai ba tare da wata rufa-rufa ba game da shirin nata.

  • INEC Za Ta Gurfanar Da Wadanda Ake Zargi Da Aikata Laifukan Zabe

Kasar Sin da ragowar kasashen duniya, na fatan Japan za ta yi matukar la’akari da damuwar sassan kasa da kasa da ma al’ummarta a cikin guda. Wani abin takaici shi ne akwai rahotannin kafofin watsa labarai dake nuna cewa, Japan ta shawo hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya game da rahotonta na karshe, mai nasaba da tsarin Japan din na zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, lamarin da ya kara sanya kasashen duniya cikin damuwa, domin rahoton hukumar ba ya nufin an amince Japan ta zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku. Wai yaro bar murna karenka ya kama zaki.

Ya kamata Japan ta fahimci cewa, zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku, daidai yake da dawo da hadarin illar nukiliya ga daukacin bil-Adama, kuma wannan matakin da kasar Japan ta dauka, ya saba wa muradun da’a na kasa da kasa, da dokokin kasa da kasa kamar yarjejeniyar MDD kan dokar teku, da yarjejeniyar London ta hana gurbatar ruwa ta hanyar zubar da sharar gida da sauran al’amura.

Masharhanta dai na bayyana cewa, abu mafi fa’ida shi ne Japan, da ta dakatar da shirinta na zubar da ruwan dagwalon a cikin teku, maimakon haka ta sarrafa shi ta hanyar kimiyya, aminci da gaskiya, ta kuma hada kai da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, don aiwatar da matakan da suka dace game da tsarin sa ido na kasa da kasa na dogon lokaci, wanda zai shafi makwabtan Japan da sauran masu ruwa da tsaki ba tare da bata lokaci ba. Haka kuma ya wajaba hukumar IAEA ta gabatar da rahotonta na nazari bisa goyon bayan kimiya da tarihi, maimakon amincewa da matsayar Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku. Ya dace Japan ta fahimci cewa, bayan kin gaskiya fa, sai bata, kuma tsalla daya ake yi a fada rijiya, amma sai an yi dubu kafin a fito.

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

Don haka, Japan tana da sauran lokaci na gyara wannan batu, don gudun dan da na sani….

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

October 15, 2025
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

October 14, 2025
Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani
Daga Birnin Sin

Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

October 14, 2025
Next Post
Kotu Ta Aike Da Wani Direban Adaidaita Sahu Gidan Gyaran Hali Kan Laifin Kisa A Adamawa

Kotu Ta Aike Da Wani Direban Adaidaita Sahu Gidan Gyaran Hali Kan Laifin Kisa A Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

October 15, 2025
Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

October 15, 2025
Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

October 15, 2025
Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

October 15, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

October 15, 2025
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu

October 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako

October 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Kama Mutum 105, Sun Ƙwato Ƙwayoyi Sama Da 5,000 A Jigawa

October 15, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara

October 15, 2025
Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

October 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.