Rikici ya ɓarke a tsakanin matasa masu haƙar zinariya da wasu Yaran Turaku a unguwar Tashar Kattai, Yauri dake jihar Kebbi, wanda ya jawo mutuwar matashi guda a daren Asabar. Lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 12 zuwa 1 na dare, inda aka ce an sari wani matashi da adda, daga bisani ya rasu a asibiti a safiyar Lahadi.
Shugaban ƙaramar hukumar Yauri, Hon. Abubakar Shuaibu Kauran Yauri, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kai rahoton mutuwar ne da misalin ƙarfe 3 ranar Lahadi. Ya ce, “Bayan bincike, an gano raunin sara ne na adda a jikinsa. Wannan ya sa muka kira jami’an tsaro daga ɓangarori daban-daban domin tattaunawa kan matakan da za a ɗauka.”
A cewar shugaban, rikicin ya sake tashi lokacin da ake jana’izar mamacin, inda wasu daga ɓangarorin biyu suka fito da adduna suna lalata kayayyaki da neman ɗaukar fansa. Lamarin ya jawo ƙona mashin guda bakwai da kuma fasa shagunan ’yan kasuwa, abin da ya tilasta kafa dokar ta baci a garin Yauri daga ƙarfe 10 na dare zuwa 7 na safe har zuwa wani lokaci.
An gudanar da taron gaggawa tare da jami’an tsaro da Sarkin Yauri, Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi, inda aka amince da dokar ta ɓaci da kuma samar da kayan aiki ga jami’an tsaro don sintiri. Kauran Yauri ya yi kira ga mazauna gari da su bi doka, tare da mika ta’aziyya ga iyalan mamacin. Ya kuma tabbatar da cewa kasuwanci zai ci gaba daga ƙarfe 7 na safe zuwa 10 na dare ba tare da matsala ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp