Sace dalibai ‘yan makarantar firamare da sakandare a Kuriga da ke Jihar Kaduna da mata da yara ‘yan gudun hijira a Gamborun Jihar Borno da kuma almajirai a Gidan Bakoso a Jihar Sokoto sun bayar da hannun agogo baya game da yunkurin da jami’an tsaro ke yi na fatattakar ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a yankin arewa.
An kiyasta cewa akalla cikin kwana 10 an sace sama da mutum 500, baya ga karin wasu da aka sace har mutum 61 a kauyen Buda da ke Karamar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.
- Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL
- Ba Za A Iya Dakatar Da Dunkulewar Kasar Sin Ba
Daliban Kuriga akalla 285 da aka sace suka fi daukar hankali saboda kananan yara ne wanda lokacin zuwa rubuta wannan labarin ‘yan bindigar suke neman a ba su fansar Naira Tiriliyan 1 kafin su sako su.
Wakazalika, ‘yan bindigar suna neman fansar Naira Miliyan 20 a kan almajirai 15 da suka sace a Sakkwato, yayin da a Jihar Borno kuma boko haram ta fara sako mata 9 daga cikin matan da ta sace sama da 200.
Garin Kuriga, daya ne daga cikin mazabu 12 na Karamar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna. Garin yana da manyan makarantun firamare guda biyu, daya ta gabas dayar kuma ta yamma. Kana akwai makarantar sakandire wacce aka samar da ita shekaru 10 da suka wuce, mai kimanin tsawon kilomita daya kamin shigowa cikin garin.
Tarihi ya nuna, Kuriga gari ne mai takama da ilimi kusan tsawon shekara 300 da suka wuce, da masarauta mai dadadden tarihi, wanda masana tarihi suka ce; ta girmi Masarautar Birnin Gwari, sannan gari ne mai kewaye da ganuwa.
Wakilinmu ya gano cewa, bullar matsalar wasu ‘yan ta’adda shekaru kamar shida da suka wuce, Kuriga ta samu kanta a wani yanayi, sakamakon idan ka taso tun daga Birnin Gwari har zuwa Kaduna, babu wanda ya fi su shan wahalar ‘yan ta’adda, wadanda suke shiga garin a lokacin da suka ga dama babu dare babu rana.
Daya daga cikin matasa kuma masu fafutukar kare hakkin Kuriga, Aminu Gwadabe ya bayyana wa LEADERSHIP Hausa cewa, lokacin da lamarin ya faru yana kan hanyarsa ta dawowa daga Kaduna.
A cewarsa, kwashe ‘yan makarantar da aka yi a halin yanzu, ba shi ne karo na farko ba, hasali ma al’ummar wannan gari; sun dade suna fama da matsalar ‘yan ta’adda, lamarin da ya kai hatta noma ba su barin su, su yi cikin kwanciyar hankali.
Aminu Gwadabe Kuriga, da ne ga Hakimin Kuriga; Alhaji Jibrin Gwadabe Kuriga, wanda a baya ya tsallake harin ‘yan ta’adda, lokacin da suka kai masa hari a gona suka harbe shi a ciki, amma daga bisani ya warke.
“Har ila yau, ‘yan ta’adda sun taba shiga cikin wannan gari namu ana tsaka da yin sallar Juma’a, suka bude wuta suka kashe mutane tare da kwashe wasu da kuma shanun kiwo; suka kama masu zuwa sana’ar gawayi da itace.
“Duk wani kauye da ke zagaye da wannan gari na Kuriga, sai da suka yi silar tashinsa, inda akalla akwai kauyuka kimanin guda goma da suka hada da Manini, Kunnama, Unguwar Barau, Janmaye, Sararai, Kufara, Tudun Tsakuwa, Gwauro, Tashar Tsuntsaye, Unguwar Rahama da kuma Unguwar Zarumai, wadannan kadan kenan daga cikin kauyukan da suka tasa “, in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Kalubalen tsaro ya ta’azzara a garin Kuriga, inda ta kai ga idan mutane za su je gona; sai su kama wasu daga cikinsu su ce sai an saya musu abinci ko an ba su kudi kafin su sake su. Ganin yadda wannan al’amari ya ta’azzara ne ya sa aka yanke shawarar cewa, wannan makaranta da ke wajen gari, malamai da sauran kafatanin dalibanta; su dawo cikin gari, wato wannan makaranta ta firamare kenan tunda tana da girma. Haka aka gwamutsa su da ‘yan sakandire tsawon shekara biyu zuwa uku, domin kauce wa faruwar abin da ya faru na rashin jin dadi a daidai wannan lokaci”.
“Wata daya da ya wuce, ‘yan ta’adda suka shigo wannan gari suka kashe Shugaban Makarantar Sakandire, Idris Abu Safiyanu har cikin gidansa, wannan ya sa an sake samun tasgaro a wannan fanni na ilimi. Ana cikin wannan jimami kuma, sai ga shi a safiyar ranar alhamis da misalin karfe takwas zuwa takwas da rabi, suka fado cikin wannan makaranta, wadda ke dauke da dalibai akalla dubu daya tare da dalibai ‘yan firamare fiye da dubu biyu, inda Allah ya kaddara suka samu nasarar kwashe dalibai 287”, a cewar ta Gwadabe.
“Har wa yau, yaran da ka ji ana cewa, wai sun dawo ba a riga an tafi da su ba ne, saboda lokacin da suka kwashi daliban wasu saboda sun firgita; ya sa suka makale a nan wasu kuma an je tsallake wani Rafi da ake kira Rafin Na- Gwanda suka buya a ciki”.
“Labari ya bayyana cewa, wadannan yara da suka shiga da su cikin daji, sun raba su ne gida biyu zuwa uku, ba a wuri daya suka bar su ba; wasu an ce an tsallaka da su zuwa hedikwatar ‘yan ta’addar da ke Zamfara, wasu kuma suna nan tsakanin Dajin Kuriga da Birnin Gwari; wasu kuma an ce an yi gabas da su ta bangaren Rijana.
“Sannan, akwai mata da yawa masu juna biyu wadanda suka yi barin cikin da suke dauke da shi, wasu kuma suna kwance a asibiti babu lafiya; ba su san inda kansu yake ba. Don haka, Garin Kuriga a halin yanzu babu kwanciyar hankali ko kadan, amma dai ana nan ana ta addu’ar Allah ya dawo da yaran nan cikin kwanciyar hankali”, in ji Aminu Kuriga.
Haka zalika, wani yaro guda da ya samu nasarar kubuta daga hannun ‘yan ta’addan; Mustapha Abubakar, ya bayyana cewa ko shakka babu, ya ga tashin hankalin da bai taba ganin irin sa ba a rayuwarsa.
“Wadannan ‘yan bindiga, sun kora mu kamar shanu, suka yi ta tafiya da mu a cikin daji; tun muna tafiya cikin hankali har sai da muka dawo muna sassarfa.”
Mustapha ya ce, ya yi tafiya mai nisa cikin gudun fanfalaki, inda ya ce ya sha azabar da bai taba gani a rayuwarsa ba, ba zai kuma taba iya mantawa da ita ba.
Ya kara da cewa ” ga jiri ina gani amma haka na daure ga kuma yamma na kawo jiki har Allah ya kai ni wani gari da ake kira Gayan, daga nan ne na kubuta daga hannunsu.”
Bayan haka, wata majiya mai tushe ta shaida wa LEADERSHIP Hausa, cewa “Jiya Talata masu garkuwa da mutanen sun kira waya suka ba da tabbacin Yaranmu suna hannunsu. Kuma sun ce an raba su wurare daban-daban ne, sun ce mana akwai wasu a yammacin Gusau wasu kuma suna Dajin Rijana wasu suna dajin Jihar Neja.
“Sun tabbatar mana da cewa gwamnati ba za ta iya karba mana yaranmu ba saboda bata shirya ba, wai idan har muna bukatar yaranmu to mu kawo kudin da suka bukata.”
Wajiyarmu ta ci gaba da cewa ” lokacin da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kai ziyara a gabansa suka kira waya suka ce yanzu haka wasu daga cikin daliban suna Jihar Zamfara a wani kauye da ke Yammacin Gusau.”
Ita dai Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen karbo yaran, sai dai wasu mutane na ganin gwamnatin ba ta yin wani abin a zo a gani yadda ya kamata kan lamarin.
A halin da ake ciki kuma, Shugaba Tinubu ya lashi takobin cewa ba za a biya ko kobo ga ‘yan bindigar da sunan kudin fansa ba domin sako dalibai da sauran wadanda suka kama.
Ya bayyana haka ne a yayin taron Majalisar Zartarwa ta wannan makon.
Da yake karin haske bayan zaman majalisar, Ministan Labarai, Mohammed Idris ya jaddada cewa, Shugaba Tinubu ya bayar da umarni mai karfi ga jami’an tsaro su dakile sabuwar barazanar sace-sacen mutane, “kuma babu batun biyan kudin fansa, saboda gwamnati ba ta goyon bayan aikata miyagun laifuka ta kowace fuska, za a ceto daliban nan da sauran wadanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.” Ya bayyana. …Mutane Gonin Gorar Kaduna Sun Dimauce Da Kudin Fansar Tiriliyan 40
A halin da ake ciki kuma, kwanaki kadan bayan sace dalibai 287 na Kuriga, sai ga al’ummar Gonin Gora, duk a cikin Karamar Hukumar ta Chikun; sun wayi gari da wani labari da ya jefa su cikin dimuwa dangane da fansar Naira tiriliyan 40 a kan mutum 16 da aka yi garkuwa da su, ranar Laraba 28 ga Fabrairun 2024.
Baya ga makudan kudin, har ila yau, ‘yan bindigar sun nemi a kai musu motocin hilus 11 da babur 150 sababbi.
A wata ziyara da wakilinmu ya kai yankin, ya tarar da mazauna garin cikin zaman zullumi da fargaba, musamman na jin sabon labarin neman kudin fansa mai matukar tayar da hankali.
Sarkin Gonin Gora, Cif John Gaza ya ce, ba zai yi magana da dan jarida ba, bisa abin da ya kira na rashin tsaron rayuwarsa.
Da yawan mutanen da suka yi magana da wakilinmu sun bayyana damuwarsu kan yawan dazuzzukan da suka hade Gonin Gora da Birnin Gwari, wanda ke zama musu barazana na ‘yan ta’adda.
Sun bukaci gwamnati ta kafa sansanin soji, wanda hakan a cewarsu zai taimaka wajen rage samun yawaitar harin ‘yan bindigar a yankin baki daya.