Shugaban kasa Bola Tinubu ya sauke Jalal Arabi daga mukaminsa na shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), sannan ya amince da nadin Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin sabon shugaban hukumar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a yammacin ranar Litinin, ta bayyana cewa, Farfesa Usman fitaccen malami ne wanda ya kammala karatu daga cibiyoyin ilimi na Islama guda biyu – Jami’ar Madina da Jami’ar Peshawar ta Pakistan.
- Adadin Masu Shigowa Da Fita Daga Sin Ya Karu A Watanni 7 Na Farkon Bana
- Babban Kwamandan Boko Haram Da Wasu Mutane 9 Sun Mika Wuya Ga Sojoji A Borno
“Har ila yau, ya kware wajen gudanar da ayyukan Hajji, bayan da ya taba rike mukamin Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kano.
“Ana tsumayin Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin.”
Ngelale ya kara da cewa, “Shugaban kasa Tinubu na sa ran sabon shugaban NAHCON zai gudanar da aikinsa bisa gaskiya, da rikon amana ga kasa.”