Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta kasa, ta fitar da sanarwar yajin aiki nan da kwanaki 21 ga Gwamnatin Tarayya idan har ba a biya mata bukatunta ba.
An fitar da sanarwar ne a karshen taron majalisar zartarwa na kungiyar, wanda aka gudanar a jami’ar Ibadan.
- Gwamnatin Adamawa Za Ta Fara Biyan Mafi Karancin Albashi N70,000 A Watan Agusta
- NYSC Ta Kori Ƴan Bautar Ƙasa 54 Masu Takardun Bogi
Yanke wa’adin, zai kara matsin lamba ga gwamnati don warware takaddamar da ke tsakanin bangarorin biyu tare da kaucewa ci gaba da kawo cikas ga cibiyoyin ilimi a fadin kasar.
Wata majiya a cikin majalisar zartaswar kungiyar ta ASUU ta kasa ta tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Litinin.
Idan dai za a iya tunawa, ASUU ta yi barazanar shiga yajin aikin a baya saboda rashin aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma da gwamnatin tarayya.
Amma a ranar 26 ga watan Yuni, Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya gayyaci kungiyar zuwa wani taron tattaunawa kan batutuwan da suka shafi jami’o’i da kuma dakile yajin aikin da suka shirya yi.
Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya yi magana kan sakamakon taron, ya ce ba a aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla da gwamnatin tarayya ba.
Talla