Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa wani kwamitin neman shawara mai mambobi 46 na fitattun malamai na addinin Musulunci, manyan malamai, da shugabannin al’umma masu daraja, wanda za su ba da shawarwari ga gwamnatin sa.
Wannan kwamitin da aka sanya masa suna “Kwamitin Shura”, an kafa shi ne domin inganta shugabanci mai tafiya tare da al’umma da kuma inganta tsarin É—aukar matakai ta hanyar haÉ—in gwuiwa da al’umma, kamar yadda kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana.
- Ma’aikacin Asibiti Ya Dawo Da Naira Miliyan 40 Da Aka Manta A Kano
- Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu Kwamishinoni 5
Kwamitin ya zo ne bayan awanni 24 daga lokacin da gwamnan ya gudanar da sauye sauye a gwamnatinsa, inda ya sallami Sakataren Gwamnatin Jihar, da Shugaban Ma’aikatar Gwamnatin, da kwamishinoni guda biyar. Duk da haka, tsohon Shugaban Ma’aikata, Shehu Wada Sagagi, ya zama Sakataren Kwamitin da zai jagoranci ayyukansa domin tabbatar da inganci da kyakkyawar hada-hadar aiki.
Kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin Farfesa Shehu Galadanci, tare da Farfesa Muhammad Sani Zahraddeen a matsayin Mataimakin Shugaba. Mambobin kwamitin sun haɗa da Sheikh Abdulwahhab Abdallah, Sheikh Ƙaribullah Nasiru Kabara, Dr. Bashir Aliyu Umar, da Sheikh Tijjani Bala Ƙalarawi, da sauran fitattun mambobi daga sassan al’umma.