Bayan kwashe shekaru 32 yana jagorantar Salloli a matsayin Limami na dindindin a Masallacin Haramin Makkah, Sheikh Saud Ash Shuraim, ya bayar da uzurin ajiye aikin Limancin.
Sheikh Shuraim, ya bukaci ajiye limancin ne bisa wasu dalilai na kashin kansa da ya bayar a matsarin uzurin jingine jagoranci sallah a Masallacin.
- Saudiyya Ta Kama Wanda Ya Shigar Da Wanda Ba Musulmi Ba Cikin Makkah
- An Cafke Wani Mutum Da Ya Daga Bana Mai Dauke Da Hoto A Masallacin Haramin Makkah
Limamin bai fito ya bayyana dalilansa na janye wa daga ci gaba da jagorancin limancin ba kawo yanzu kamar yadda kafar yada labarai na Haramaini Sharifain ya bayyana.
Sai dai ko da yake bayanai sun bayyana cewa malamin zai iya komawa limancin jagorancin Sallar Tarawihi a matsayin bakon limami wanda za a sanar da hakan nan da makonni masu zuwa.