A karon farko bayan shekara 1993, Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta samu nasarar sahalewar kara karbar harajin da ya kai kashi 15.
Wannan matakin na sahalewar, an yi ne, bisa nufin samar da sabbin kayan aiki da fadada Tashar Jiragen Ruwa.
Shugaban Hukumar, Dakta Abubakar dantsoho ya bayyana cewa, sake sabunta biyan harajin, zai taimaka wajen yiwa Tashar Jiragen Ruwan garanbawul, samarwa Tashar kayan aiki na zamani da kuma samar da kayan samar da bayanai, na kimiyyar zamani wato ICT.
- Yara Miliyan 1 Ke Mutuwa Duk Shekara A Farkon Watansu Na Haihuwa A Nijeriya – UNICEF
- NLC Ta Buƙaci Gwamnatin Tinubu Ta Soke Sabuwar Dokar Haraji
Kazalika, dantsoho ya sanar da cewa, sabunta biyan harajin, zai kara samarwa da Tashar kudaden shiga, marawa ayyukan da ake yi baya, ciki har da ayyukan garanbawul na Escrabos Breakwaters da gyran Tashoshin Jiragen Ruwa na jhar Ribas, Onne, da kuma na garin Kalaba.
Masu ruwa da tsaki a fannin sun yi maraba da karin biyan harajin, inda suka yi nuni da samun hauhawan farashi, wanda a yanzu, ya kai kimanin kashi 34.8 da kuma samun karauwar tsadar kayan aiki.
Shi kuwa tsohon Janar Manaja na Hukumar ta NPA Joshua Asanga, ya jaddda mahimmancin amincewa da karin biyan harajin wanda ya sanar da cewa, sahalewar za ta taimaka wajen samar da kayan aiki a Tashar Jiragen Ruwan, inda kuma shi ma wani mai ruwa da tsaki a fannin ya yi kira da a zuba hannun jari a wasu bangarori na Tashar.
Mahukunta a bangaren tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa a fadin duniya, sun dogara ne, wajen samar da kudaden shiga domin su samu damar ci gaba da kula da kayan gudanar da ayyukansu da kuma kara tabbatar da tsaro, a Tashohin Jiragen Ruwan su.
Bugu da kari, wasu kararru a fannin sun bayyana cewa, harajin da Hukumar NPA ke karba shi ne mafi karanci a yankin.