Al-Waleed bin Khaled bin Talal Al Saud, wanda aka fi sani da Yarima mai Bacci na Saudiyya’, ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe kusan shekaru ashirin yana dogon bacci. Ya rasu yana da shekaru 36.
Ya rasu ne a Asibitin King Abdulaziz Medical City da ke Riyadh a ranar Asabar, inda kafin rasuwar tasa yake amfani da na’urar taimakon numfashi tun bayan mummunan haɗarin mota da ya yi a Landan a shekarar 2005. A lokacin, yana karatu a kwalejin Soja a Birtaniya lokacin da hatsarin ya faru, wanda ya haifar masa da munanan raunuka a kwakwalwa.
- Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya
- Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Saudiyya Don Halartar Jana’izar Ɗantata
Ƴansandan mahaifinsa sun tabbatar da mutuwar nasa ta hanyar wallafa sakon alhini a kafafen sada zumunta.
“Da zuciya mai amincewa da ƙaddara da hukuncin Allah, muna sanar da mutuwar ɗanmu abin ƙauna: Yarima Al-Waleed bin Khaled bin Talal bin Abdulaziz Al Saud. Allah ya jiƙan sa, ya gafarta masa,” in ji mahaifinsa cikin alhini.
Gidan Sarautar Saudiyya ya tabbatar da rasuwar, inda ya sanar da cewa za a gudanar da Sallar jana’iza a ranar Lahadi, 20 ga Yuli, a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke Riyadh bayan Sallar La’asar.
Tun bayan haɗarin, labarin lafiyarsa ya janyo hankalin mutane da dama. Sau da dama yana yin ƙananan motsi na hannu ko kai, wanda ke ƙara ƙarfafa fatan iyalansa da al’ummar da ke ƙaunarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp