Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar birnin New York na Amurka, bayan kammala wakiltar Shugaba Bola Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA). Ya nufi Jamus domin ganawa da jami’an Bankin Deutsche kan batutuwan haɗin gwuiwa da zuba jari a shirye-shiryen ci gaban Nijeriya.
A yayin taron UNGA, Shettima ya samu yabo daga Sakatare-Janar na MDD, António Guterres, bisa ƙoƙarin Nijeriya na neman kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro. Haka kuma ya gabatar da damar zuba jari a fannin makamashin mai darajar dala biliyan 200, tare da ƙarfafa haɗin gwuiwa da Birtaniya kan harkokin kasuwanci da tsaro da kuma ƙaura (ci rani).
- Gwamna Yusuf Ya Aike Da Sunayen Kwamishinoni Zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano
- UNGA: Tinubu Ya Nemi Kujerar Dindindin Ga Nijeriya A Majalisar Tsaro
Ya kuma jaddada buƙatar garambawul a Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya buƙaci a baiwa Afrika ikon sarrafa arziƙin ma’adanan da darajarsu ta kai dala biliyan 700. Shettima ya kuma tattauna da gidauniyar Gates kan faɗaɗa kiwon lafiya da ilimi, kana ya jawo hankalin masu zuba jari kan kasuwar dala tiriliyan 3.4 na African Continental Free Trade Area (AfCFTA).
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bar filin jirgin sama na John F. Kennedy (JFK) inda ministoci da jami’an ofishin jakadancin Nijeriya suka raka shi. An tabbatar da cewa zai dawo gida kai tsaye bayan kammala aiyukansa a Jamus.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp