Kasa da ‘yan awanni da cire mahaifinta daga sarautar Wazirin Bauchi, Kwamishiniyar ma’aikatar kasuwanci da masana’antu ta jihar Bauchi, Hajiya Sa’adatu Bello Kirfi ta yi murabus daga mukaminta.
Sa’adatu a wata wasikar da ta aike wa gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad mai kwanan wata 4 ga Janairun 2023 ta ce ajiye aikin nata ya fara aiki ne nan take.
Daga bisani ta gode wa gwamnan Jihar a bisa ba ta damar zama daga cikin mambobin Majalisar zartaswa ta jihar.
Duk da ya ke dai ba ta yi bayanin dalilan da suka sanya ta ajiye mukamin nata ba, ana ganin bai rasa nasaba da korar mahaifinta Alhaji Muhammad Bello Kirfi daga Sarautarsa ta Wazirin Bauchi ba bisa abun da aka misalta rashin biyayya da rashin mutunta gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad da aka sameshi da yi.
A wasikar tsige Bello Kirfi daga mambar Majalisar masarautar ta Bauchi mai dauke da kwanan wata Talata 3 ga watan Janairun 2023 dauke da sanya hannun sakataren masarautar, Alhaji Shehu Mudi Muhammad da wakilinmu ya ci karo da ita.
Wani bari na wasikar na cewa, “An umarceni da na koma ga wasikar da aka samu daga ma’aikatar kananan hukumomi da kula da harkokin masarautun gargajiya mai lamba MLG/LG/S/72/T da ke dauke da kwanan wata 30 ga watan Disamban 2022.”
“Wasikar na kunshe da cewa ba ka biyayya da mutunta mai girma gwamnan Jihar Bauchi da Gwamnati. Kan hakan an umarci a cire ka nan take.
“Bisa bayanan da suke a sama, an cireka daga ofis a matsayin Wazirin Bauchi kuma mamba a cikin Majalisar masarautar Bauchi”.
Alhaji Shehu Mudi Muhammad daga bisani ya yi wa korarren Wazirin Bauchi fatan alkairi a rayuwarsa ta gaba.
LEADERSHIP Hausa ta yi tilawar cewa shi dai Wazirin Bauchi, Alhaji Muhammad Bello Kirfi an taba dakatar da shi daga sarautarsa a zamanin mulki gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar wanda Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu ya yi a watan Maris na 2017.
Bayan da gwamna Bala Muhammad Abdulkadir ya zama gwamna a 2019 ya shiga ya fita har aka samu nasarar sake dawowa Muhammad Bello Kirfi da Sarautarsa, yanzu kuma an koreshi gaba daya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp