Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce, ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki kashi 85 cikin 100 da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke yi ya ƙara nuna gwamnatin a matsayin dimokiraɗiyya mai son jama’a.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a jawabin sa na buɗe Taron Ministoci Karo na 4 a Cibiyar ‘Yan Jaridu ta Ƙasa da ke Abuja.
- 2023: Manyan Jiragen Ruwa 75,000 Suka Yi Hada-hada A Tashar Lekki
- Yau Za A Yi Mugun Zafi Mai Haɗari A Abuja, Sakkwato, Kano Da Kogi, In Ji NiMet
Ministan ya ce: “A kwanan baya, Gwamnatin Tarayya ta fitar da wani tsari na cigaba a fannin samar da wutar lantarki, wanda ke da nufin bunƙasa wadatar wutar lantarki ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya.
“Wani muhimmin al’amari na wannan tsarin shi ne gwamnatin Tinubu na ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ga kashi 85 na masu amfani da wutar lantarki a Nijeriya, wanda hakan ya sake tabbatar da matsayin gwamnatin dimokaradiyya mai son jama’a tare da yin ƙarin kuɗin wutar lantarki ga kashi 15 na masu amfani da wutar lantarki kawai.”
Tun da farko, Ministan ya bayyana nasarorin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu ta samu a baya-bayan nan. A cewar Idris, “Tun bayan ganawar da muka yi da ku (’yan jarida) na baya-bayan nan an samu gagarumar nasara a tattalin arziƙinmu, kasancewar dukkanmu shaida ne kan yadda ta hanyar aiwatar da wasu sauye-sauye na tattalin arziƙi, kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasar waje ta daidaita, sannan kuma naira yana samun ƙarfi kullum.
“Kafa Majalisar Daidaita Tattalin Arziƙi da Tawagar Gudanar da Tattalin Arziƙi na Shugaban Ƙasa na kwanan nan ya jaddada ƙudirin Shugaban Ƙasa don samar da wani tsari mai muhimmanci na gudanar da tattalin arziƙi wanda ke yin amfani da ƙwarewa da fahimtar manyan masu ruwa da tsaki daga ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu. Waɗannan ƙungiyoyin za su zama dandamali don tattaunawa mai ƙarfi, bincike, da yanke shawara don haɓaka ci gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa, samar da ayyukan yi, da wadata ga dukkan ‘yan Nijeriya.
“Ƙaddamar da Asusun Raya Gine-gine na Sabunta Fata (RHIDF) yana da niyyar tara kusan naira tiriliyan 20 don saka hannun jari a sassa masu muhimmanci kamar su tattalin arziƙi, sufuri, noma, da Fasahar Sadarwar Bayanai (ICT) da sauransu.
“Asusun yana neman tallafawa ayyukan da ke haɓaka ci gaba, samar da guraben aikin yi, da haɓaka fitar da kayayyaki zuwa ketare.”
Idris ya ƙara da cewa, “Ayyukan da asusun zai sa a gaba sun haɗa da gina babbar hanyar Legas zuwa Calabar da aka fara kwanan nan, titin Sokoto zuwa Badagry, Legas zuwa Kano, hanyar jirgin ƙasa na Gabas da zamanantar da tashoshin jiragen ruwa da na jiragen sama a faɗin ƙasar.
“Don faɗaɗa hanyoyin samun ilimi a matsayin makamin yaƙi da talauci, Shugaban Ƙasa ya sanya hannu kan ƙudirin dokar Lamunin Ɗalibai ta 2015, ta zama doka. Wannan yunƙurin ya wuce doka kawai – hanya ce ta juyin juya hali don kafa tsari na dindindin wanda zai tallafa wa neman ilimi daga matasanmu.