Shugaban ƙungiyar masu fafutukar kawo adalci a Jihar Sakkwato, Basharu Altine Guyawa Isa, ya bayyana cewa labarin cewa ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ya ajiye makamansa ba gaskiya ba ne.
Guyawa, ya ce Turji bai amince da yin sulhu da kowa ba, kuma ba a san inda labarin cewa ya ajiye makamai ya fito ba.
- Sojoji Sun Kama Mai Yi Wa Boko Haram Safarar Man Fetur A Borno
- Remi Tinubu Ta Bai Wa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa A Neja Tallafin N1bn
A cewarsa, bindiga ce kaɗai za ta sa Turji ya haƙura da ta’addanci.
Ya ce: “Ƙasarmu ɗaya ce, yankinmu ɗaya, mu muna da masaniyar abubuwan da Turji ke yi. Idan an ce ya ajiye makamai, to wa ya bai wa? Kuma a kan wane sharaɗi ne?”
Guyawa ya ƙaryata ikirarin wani malami mai suna Sheikh Musa Assadus-Sunna da ya ce Turji ya ajiye makamai.
Ya ce malamin bai fi Sheikh Ahmad Gumi ba, wanda ya gaza yin zaman sulhu da Turji.
Guyawa, wanda ya daɗe yana taimaka wa jami’an tsaro da bayanai, ya ce ba a taɓa yin sulhu da mutum yayin da yake ci wa jama’a zarafi ba.
Ya ce: “Za a iya cewa mutum ya yi sulhu alhali yana ci gaba da karɓar haraji daga hannun manoma da tilasta musu noma? Ko kuma yana kashe mutane da ƙond motar jami’an tsaro?”
Guyawa ya ƙara da cewa Turji da sauran ‘yan ta’adda kamar Kachalla Choma da Kachalla Haru suna da makamai da kwamandoji da yawa, kuma babu wani abu da ke nuna sun ajiye makamansu.
Ya ce malamin da ya faɗi cewa Turji ya ajiye makami bai san yankin ba, kuma bai san halin da ake ciki ba.
A cewarsa, a kwanakin baya ma Turji ya kashe jami’an tsaro tare da ƙone motarsu.
Ya ƙara da cewar idan da gaske ya yi sulhu, da ba zai aikata haka ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp