Dan wasan baya na kungiyar kwallaon kafa ta Arsenal, Ben White, ya koma atisaye tare da kungiyar bayan da ya bar sansanin Ingila a Katar kan dalili na kashin kansa kamar yadda tawagar ta bayyana.
White bai yi wa Ingila wasa biyu na farko a cikin rukuni na biyu a gasar kofin duniya ba, bai kuma buga wasa da ta ci Wales ba, saboda rashin lafiya, sai dai hukumar kwallon kafa ta Ingila ce ta sanar da cewar White mai shekara 25 ya bar Katar kwana daya a fafatawa da Wales.
Sauran da suka koma atisaye a Arsenal sun hada da dan kwallon tawagar Ghana, Thomas Partey da dan wasan Amurka, Matt Turner.
Kungiyar Arsenal wadda Mikel Arteta ke jan ragama tana Dubai, inda ta buga wasan sada zumunta da AC Milan ranar Talata.
Rahotanni sun ruwaito cewa White baya jin dadi zaman da yake a sansanin Ingila, sannan ya samu sabani da mataimakin koci, Stebe Holland kuma kafin wasan daf da na kusa da na karshe da Faransa ta fitar da Ingila da ci 2-1 ranar Asabar. Gareth Southgate ya ce Ben ya bar sansanin Ingila kan dalilai na kashin kansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp