Da alama Karim Benzema ya yi ritaya daga buga wa kasarsa wasa bayan rashin nasarar da ta yi a gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar, a wasan karshe.
Karim Benzema ya bayyana alamun ritayarsa ne a shafinsa na twitter, inda yace “Na yi kokari, kura-kuraina suka kawo ni abinda na zama yau a duniya kuma ina alfahari da hakan! Na kafa tarihi kuma yau tarihin ya tsaya haka”
Benzema yana daga cikin ‘yan wasan kasar Faransa da aka zaba zasu buga wa kasar wasanni a gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Qatar ta 2022 amma raunin da yake fama da shi ya hana shi samun damar zuwa buga wasanni a gasar.
Sabida wannan raunin, Benzema bai samu damar zuwa koda kallon wasannin ba sai dai ta talabijin har kasarsa ta kai wasan karshe da Argentina amma ta sha kashi a bugun fanareti bayan tashi wasa kunnan doki 3:3.