Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jarida game da sakon taya murnar ranar kafuwar sabuwar kasar Sin da shugaban Amurka Joe Biden ya aikawa shugaba Xi Jinping a jiya Asabar.
Yayin taron manema labarai, wani dan jarida ya ce rahotonni sun ruwaito cewa, shugabannin kasashe da jam’iyyu da kuma kungiyoyin kasa da kasa da dama sun aika sakwanni ko wasiku ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, don murnar cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Shin ko shugaban Amurka Joe Biden ma ya aike da irin wannan sako?
Da yake amsa tambayar, kakakin ya ce, a kwanan nan, shugaban Amurka Joe Biden ya aika sako ga shugaban Sin Xi Jinping, don taya murnar cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Inda shugaba Biden ya bayyana cewa, a lokacin cika shekaru 75 da kafuwar sabuwar kasar Sin, shi da al’ummar Amurka, suna taya shugaba Xi da al’ummar Sin murna, tare da yi musu kyakyawan fata.(Safiyah Ma)