Da yammacin Litinin din nan ne, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya kira wani taron manema labarai don yin bayani kan halin da ake ciki a bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa na kasar Sin karo na 3.
Mataimakin ministan ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Sheng Qiuping ya nuna cewa, bikin da ake yi a wannan karo ya nace ga samar da kayayyaki masu inganci, da zummar kafa wani dandali mai karfi wajen baje kolin kayayyakin masarufi, wanda zai taka rawa wajen farfado da sayayya da biyan bukatun zaman rayuwar jama’a.
Bikin na wannan karo, ya hallara tambura masu inganci fiye da 3100. Alkaluman kididdiga na nuna cewa, fiye da tambura 300 za su gabatar da kayayyakinsu sama da 1000 a karon farko a bikin. Ban da wannan kuma, lardin Hainan zai gabatar da ayyuka irin daban-daban na samar da rangwame ga masu sayayya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp