• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bikin Bazara Na Gargajiyar Kasar Sin Ya Kara Azama Kan Farfadowar Tattalin Arzikin Duniya

by CMG Hausa
3 years ago
Chinese tourists arrive at Ngurah Rai international airport in Bali, Indonesia on Sunday, Jan. 22, 2023. A direct flight from China landed in Indonesia's resort island of Bali for the first time on Sunday in nearly three years after the route was cancelled due to the pandemic.  (AP Photo/Firdia Lisnawati)

Kwanan baya, mahukuntan kasar Sin sun gabatar da alkaluman tattalin arziki dangane da lokacin hutun bikin Bazara na gargajiyar kasar Sin na bana.

Yawan wadanda suka yi bulaguro a cikin gidan kasar Sin ya kai miliyan 308, wanda ya karu da kashi 23.1 bisa dari kan na bara. Kana yawan kudaden shiga da aka samu a fannin yawon bude ido a cikin gida a lokacin hutun na tsawon mako guda, ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 375.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 55.52, wanda ya karu da kashi 30 cikin dari kan na bara. Sa’an nan kuma yawan kudaden tikitin kallon fina-finai a lokacin hutun ya kai yuan biliyan 6.758, wanda ya karu da kaso 11.89 kan bara. Yawan wadanda suka shiga kasar Sin daga ketare da zuwa ketare daga kasar Sin kuma ya karu da kaso 120.5 kan shekarar 2022.

  • Xi Jinping Ya Gabatar Da Sakon Bidiyo Ga Taron Koli Karo Na 7 Na Kungiyar Kasashen Latin Amurka Da Caribbean

Bikin Bazara na bana, shi ne irinsa na farko, tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da sabbin matakin yaki da cutar COVID-19. Zirga-zirgar mutane sun samu farfadowa cikin sauri a kasar Sin. Alkaluman sun nuna kuzarin kasar Sin na yin sayayya.

Haka zalika an samu karin mutane da suka yi murnar bikin Bazara a ketare. Alkaluma sun nuna cewa, kwagilolin da mutanen Sin suka daddale kan yin bulaguro a ketare a lokacin hutun bikin Bazara a bana ya karu da kaso 640 bisa na shekarar bara.

A rana ta farko ta shekarar Zomo kuma, an shirya kasaitaccen bikin maraba da jirgin sama na farko a bana dake dauke da masu yawon shakatawa na kasar Sin a tsibitin Bali na kasar Indonesia, lamarin da kafofin yada labaru da dama suka watsa labaru a kai. Wasu kafofin yada labaru na kasashen waje sun yi nuni da cewa, miliyoyin masu yawon shakatawa na kasar Sin za su kara azama kan farfadowar otel-otel, aikin yawon shakatawa da kasuwanci na duniya.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Yanzu haka ana fuskantar sauye-sauye a duniya. Kasar Sin ba ta aza harsashi sosai wajen farfado da tattalin arziki ba. Tana bukatar kara yin kokarin farfado da tattalin arzikinta.

Amma al’ummar Sin na da imani da kuma kwarewa wajen farfado da tattalin arzikin kasar a shekarar 2023 da ake ciki. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Next Post
Mataimakin Wakilin Kasar Sin Dake MDD Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Taimakawa Mali Kara Karfin Yaki Da Ta’addanci

Mataimakin Wakilin Kasar Sin Dake MDD Ya Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Taimakawa Mali Kara Karfin Yaki Da Ta’addanci

LABARAI MASU NASABA

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

October 25, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.