Kwanan baya, mai sayar da tikiti na tashar jirgin kasa mai saurin tafiya ta Hongqiao da ke birnin Shanghai You Yuan ta yi suna ta kafar yanar gizo saboda kwarewarta wajen aiki, baki daga kasashen waje na yaba mata matuka kan hakan. You Yuan na daya daga masu sayar da tikiti a bangaren zirga-zirga na birnin Shanghai, wadanda suke kokarin kara kwarewarsu don hidimtawa bakin kasashen waje dake ta karuwa a birnin.
Birnin Shanghai mai bude kofa sosai ya kan zama zangon farko da baki da yawa da suke zuwa nan kasar Sin tun bayan da Sin ta fara kokarin habaka manufar ta shigowa kasar ba tare da biza ba. Alkaluman da hukumar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta birnin Shanghai ta samar sun shaida cewa, a shekarar bara, yawan baki masu yawon shakatawa da suka shigo kasar Sin da birnin ya karba ya zarce sau miliyan 6.7, adadin ya karu da kashi 84% kan makamancin lokaci na 2023.
- Shugaban Kasar Sin Ya Mika Gaisuwar Sabuwar Shekara Ga Dukkan Jami’an Tsaro
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Gudanar Da Liyafar Sabuwar Shekara
Ba da dadewa ba, za a fara bikin bazara a nan kasar Sin, wato bikin sabuwar shekara ga al’ummar kasar bisa kalandarsu ta gargajiya. Bikin na bana kuma ya kasance na farko tun bayan da UNESCO ta shigar da shi cikin jerin sunayen al’adun gado na duniya. Ba shakka, kasar Sin za ta kara samun baki daga kasa da kasa, musamman wadanda suke son fahimtar al’adun gargajiya na bikin bazara. Don haka, a biranen Sin da yawa ciki har da Shanghai, za a ga yadda Sinawa da baki da suke shagulgulan wannan biki tare.
Kamar yadda shugaban kwalejin nazarin harkokin yawon shakatawa na kasar Sin Dai Bin ya fada, farfadowar kasar Sin da Sinawa da ke more rayuwarsu na jawo hankalin al’ummun duniya sosai. Sin mai bude kofa ga duniya na maraba da zuwanku, don ganewa idonku yadda Sinawa da yawansu ya kai biliyan 1.4 suke hadin gwiwarsu wajen zamanantar da kasarsu. (Mai zane da rubutu: MINA)