Bikin bazara shi ne biki mafi dadewa da muhimmanci a bukukuwan gargajiya na Sin. Kuma bikin na ci gaba da kara bazuwa da samun karbuwa a fadin duniya.
A kwanakin baya-bayan nan, kasashe da hukumomin kasa da kasa da dama sun gudanar da shirye-shirye da nune-nunen dake da alaka da bikin bazara, kuma jama’a a fadin duniya sun hadu domin a dama da su cikin bikin murnar sabuwar shekarar ta Sin. A wannan lokaci, 1 bisa 5 na al’ummar duniya ne ke murnar bikin ta mabanbantan hanyoyi, lamarin da ya mayar da bikin bazara zuwa wata al’adar gargajiya ta duniya tare da inganta fahimta da abota tsakanin jama’ar dukkan kasashe.
- Alkaluman Watsa Shirye-Shiryen Shagalin Bikin Bazara Na CMG Na 2025 Sun Kai Sabon Matsayi
- Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Gudanar Da Binciken Lafiya Kyauta A Karkarar Sudan Ta Kudu
Hakan ba ya rasa nasaba da yadda al’adar ta taba kowanne bangare na rayuwa da kuma sakonnin da take dauke da su kamar na kyautata zumuncin iyali da girmama manya da tausayawa yara, wanda abubuwa ne dake da saukin fahimta ga jama’ar dukkan kasashe. A lokacin guda, ta hanyar bikin bazara, duniya ta ga kasar Sin dunkulalliya mai bude kofa, haka kuma ta shaida nasarorin da kasar ta samu wajen zamanantar da kanta.
Sinawa na mika fatansu na ban kwana da tsohuwar shekara da maraba da sabuwa ga duniya ne ta hanyar bikin bazara. Bikin bazara ba na Sin ba ne kadai, na daukacin duniya ne. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp