A kwanan ne aka kamala bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 7 wanda ya kasance daya daga cikin manyan hikimomin da kasar Sin ta bullo da su a karkashin shirinta na kara bude kofar hulda da sauran sassan duniya.
Na kalla ta talabijin yadda wasu mahukunta da shugabannin kamfanoni da na ’yan kasuwa daban-daban na kasashen duniya daga wasu sassan da ba na Afirka ba suke bayyana alfanun wannan biki ga ci gabansu. Abin ya zama gwanin ban-sha’awa amma dai, tun da ban yi katarin ganin na Afirka ba sai na ba zama tare da raba na-mujiya a kafafen yada labarai don zakulo yadda mutanenmu suka shiga aka dama da su.
- Salon Zamanantarwa Irin Na Kasar Sin Riba Ce Ga Duniya Baki Daya
- Ya Kamata Rungumar Hadin Gwiwa Da Yin Komai A Bude Su Zamo Ginshikan Ci Gaban Yankin Asiya Da Pacifik A Nan Gaba
Watakila mai karatu ya ce, me ya sa na damu da sai na ga na Afirka, e, dole na damu, domin na ji cewa a bisa karamci, matakan inganta harkokin kasuwanci da kasar Sin ta dauka sun kara habaka kayayyakin da Afirka ke fitarwa zuwa kasuwanninta ainun. A cikin watanni 9 na farkon bana, kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga Afirka sun kai adadin yuan biliyan 626.74 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 87, wanda ya nuna an samu karuwar kashi 10.3 cikin 100 a mizanin da ake aunawa duk shekara, kamar yadda hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayyana. Ka ga kuwa dole na bibiyi na mutanenmu na gani tun da an ce “da arziki a gidan wasu, gwara a gidanku.”
Daga shawagin da na yi a kafafen labarai, na yi kicibis da tsokacin da ’yan Afirka da suka halarci bikin baje kolin na CIIE na bana suka yi. Wani dan Nijeriya, Usman Sa’id Sufi, bayan jinjina wa kasar Sin a kan yadda take bude kofofinta ga daukacin duniya bisa adalcin kasuwanci, ya ce, a bana sun baje hajojinsu na Nijeriya da suka kunshi kayan noma da ma’adanan kasa. Yana mai cewar, “mun kawo kamar ridi, da sobarodo (ganyen zobo), kwallon tafasa, garin rogo, gyada, cashew (yazawa), karo, waken suya da sauran kayayyaki kala-kala.”
Daga kasar Afirka ta Kudu kuwa, wani dan kasuwa da ya halarci bikin a karon farko tare da baje kolin kayan lambu na avocado, Nkateko Khoza ya bayyana cewa kasuwar kasar Sin za ta kawo sabbin damammaki na bunkasa masana’antar avocado ta kasar Afirka ta Kudu, inda ya kara da cewa, wannan damar za ta bai wa kamfaninsu na noma mai suna Khoza Farming damar ninka ci gaban da yake samu a cikin shekaru uku zuwa biyar masu zuwa.
Wani abin ban-shawa da ke kara nuna yadda Afirka ke shiga a dama da ita a kasuwar baje kolin ta CIIE shi ne, wannan ne karo na farko da ake baje kolin naman kosassun raguna na kasar Madagascar. Amma kafin nan, kasar Sin ta riga ta shigo da irin wannan naman na farko daga Afirka a watan Satumbar bana, bayan da hukumar kwastan ta Changsha da ke tsakiyar kasar Sin ta tantance ingancin naman na Madagascar. A cewar Babban Daraktan Noma da Kiwo na Ma’aikatar Noma ta Madagascar, Michel Anondraka, babbar kasuwar kasar Sin za ta bunkasa harkokin noma da kiwo ga manoman gida, tare da gaggauta zamanantar da aikin gona na yankin Afirka.
Haka nan duk dai a bikin na CIIE na bana ne aka fara baje kolin zumar da kasar Tanzaniya ke samarwa. Kuma bisa yakinin Babban Manajan Kamfanin Sarrafa Zuma da Samar da Kayayyakin Kiwonsa na Tanzania Future Enterprises Company Limited, Jackson Mponela, “Wannan baje kolin wata babbar dama ce ga harkokin kasuwancin zuma a fadin Tanzaniya, domin ba wai kawai ya share fagen shiga kasuwannin kasar Sin ne kadai ba, har ma ya zama wani muhimmin mataki ga cinikayyar zumar Tanzaniya a kasuwannin duniya.”
Wadannan kadan ne daga cikin misalan kara shigowar Afirka a dama da ita a bikin baje kolin CIIE na bana kuma tabbas, karamcin da kasar Sin ta yi wa kasashen Afirka 33 da suke huldar diflomasiyya tare cewa ta cire musu harajin halartar kasuwar baje kolin, zai kara musu kaimi da kuma cin moriyar juna.
A kalla shugabannin gwamnatoci da kamfanoni da kungiyoyin ’yan kasuwa daban-daban na duniya 77 ne suka halarci bikin baje kolin na CIIE na bana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)