An bude bikin baje kolin inganta tsarin samar da kaya na kasa da kasa na Sin, wato bikin CISCE karo na farko a ranar 28 ga watan nan a birnin Beijing, wanda ya jawo hankalin kamfanoni masu yawa na Amurka da kasashen Turai, kuma yawansu ya zarce hasashen da aka yi, inda ya kai kashi 36 cikin dari bisa jimillar ’yan kasuwar ketare da suka hallarci baje kolin.
A cikin kwanaki 5 da za a yi ana gudanar da baje kolin, kamfanoni fiye da 500 daga kasashe da yankunan duniya 55, sun nuna sabbin fasahohin zamani, da kayayyaki, da kuma hidimomi na tsarin samar da kaya daban daban.
- Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Kashi 91.4 Sun Yaba Da Gudummawar Sin Kan Tinkarar Sauyin Yanayi
- Xi Ya Kai Rangadin Aiki A Birnin Shanghai
Abin da aka lura shi ne, a cikin wasu awoyi da suka gabata kafin bude baje kolin, fadar White House, wato gwamnatin kasar Amurka ta gudanar da wani taro game da tsarin samar da kaya, ta kuma sanar da kafa “kwamitin kula da tsarin samar da kaya”, kana ta kaddamar da tsarin gargadi game da katse samar da sassan kayan laturori na “semiconductor” gaba daya, da sa kaimi ga samar da magunguna masu mahimmanci a cikin gidan Amurka da sauransu. Amurka ta yi ikirarin cewa wadannan matakan suna da mahimmanci ga tattalin arzikinta, da kuma tsaron kasa, amma a idon sassan waje, hakan matakin ba da kariya ne da gwamnatin Amurkan ta kan dauka, inda a zahiri take yunkurin dakile ci gaban kimiyya da fasahar Sin, da kuma rage dangantakar tattalin arziki tsakaninta da Sin.
Amma a fannin kasuwanci, bikin CISCE ya jawo hankalin kamfanonin Amurka da kasashen Turai, wanda ya nuna cewa, matakan siyasa ba za su iya canza ka’idojin kasuwa ba, kuma ba zai yiwu a cire kasar Sin daga cikin tsarin samar da kaya a duniya ba.
Yayin wannan baje koli na tsarin samar da kaya, kalaman shugaban Indonesiya Joko Widodo, sun tunatar da mutane bukatar shiga a dama da su wajen gina hadin gwiwar tsarin samar da kaya a duniya, maimakon masu muguntawa. Alkaluma sun tabbatar da cewa, “kasar Sin” ta nan gaba za ta kasance kasar Sin, wannan shi ne ainihin dalilin da ya sa kamfanonin kasashen Turai da Amurka ke kokarin tafiya tare da ita. (Mai Fassarawa: Safiyah Ma)