Sabuwar shekarar Sinawa bisa kalandar gargajiya ta kasar, tana alamta shigowar sabuwar arziki cikin al’umma a sabuwar shekara. Bikin wannan sabuwar shekarar tana lale marhabin da kwazo, da kuzari, da nasara. Wannan takaitaccen bayani ne game da tarihin Sabuwar Shekarar gargajiya ta Sin, da lakabin da aka yiwa shekarar ta dabbar “Loong” da al’adun da ake girmamawa don murna da jin dadin hutun sabuwar shekara.
Mece ce Sabuwar Shekarar Sinawa?
Sabuwar Shekarar Sinawa tana faduwa a kan ranaku daban-daban a kowace shekara bisa kalandar gargajiyar kasar. Asali, wannan biki nuna girmamawa ce ga kakanni da ababen bauta, wanda a kan shafe kwanaki 15 ana gudanarwa kuma yana karewa da cikar wata na farkon shekara.
Ana nasabta ma’anar alamun taurari na kasar Sin ga daya daga cikin dabbobi goma sha biyu a kowace shekara. Wannan al’adar ta samo asali ne daga wata tsohuwar waka ta kasar Sin da ta ba da labarin dabbobin tatsuniyoyi 12 da suke saukowa daga sama don kawo damina da sabon girbi. Wannan shekara ta 2024, ita ce shekarar dabbar Loong. Baya ga alamar tauraro ta dabbar, kaza lika sabuwar shekara ta Loong tana dauke da daya daga cikin alamun abubuwa biyar masu muhimmanci a duniya, wato kasa, itace, wuta, karfe, da ruwa. Wannan shekara ta 2024, na daukar alama ta biyu wato itace, hakan ya sanya shekarar kasancewa ta dabbar Loong ta itace.
Muhimmancin Shekarar Dabbar Loong
Don fahimtar mahimmancin kowace sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa, yana da muhimmanci mu fahimci yanayin mu’amalar wadannan alamun taurari na dabbobi da kuma alamun abubuwa biyar masu muhimmanci da na ambato a baya. Ga wannan shekarar ta Loong, yana da mahimmanci mu fahimci halayen itace da ma dabbar Loong. La’akari da itace a matsayin alama ta sabuwar shekarar Sinawa ta 2024, yana nuni da girma, nasara, da matakin farko na ci gaba. Itace alama ce ta burin dan adam da yake son ya cimmawa, kamar, ci gaba, girma, da fadadawa. Ita kuma alamar dabbar Loong tana wakiltar lafiya, karfi, da sa’a. An yi imanin cewa wadanda aka haifa a wannan shekara suna dauke da halayen da ke da alaka da dabbar dake alamta jagoranci na halitta, kwarjini, da sha’awa mara iyaka.
Al’adun da ake girmamawa a lokacin bikin sabuwar shekara.
Daga cikin al’adun da ake girmamawa a lokacin bikin sabuwar shekarar Sinawa akwai bayar da kyaututtuka a cikin jajayen ambulaf, dattawa suna ba da kyautar kudi a cikin jajayen ambulaf, wanda ake ce ma “hongbao”, ga yara da jikoki don nuna fatan samun arziki mai amfani a shekara mai zuwa. Sukan sanya kudi a cikin wadannan ambulaf din, wanda ke nuna alamar kyakkyawar fatan shiga sabuwar shekara. Bayan dattawa, abokan aiki da aminai su ma sukan yi musayar hongbao. Akwai kafafe da dama na isar da hangbao zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki kamar ta lalitar kudi na manhajojin wechat da alipay.
Wasan Wuta da kunna fitilu
Babu murnar bikin sabuwar shekara da aka yi ba tare da gudanar da gagarumin wasan wuta da kunna fitilu ba. Kowace shekara, fitilu suna haskakawa don korar duhu da haskaka bege na shekara mai zuwa. Wannan tsohuwar al’adar ta samo asali ne fiye da shekaru 2,000 daga daular Han, kuma ta kasance wani muhimmin bangare na bukukuwa a kasar Sin musamman bikin sabuwar shekara. A kan saki fitilu zuwa sararin sama a daren karshe na bikin kwanaki goma sha biyar.
Sake haduwa da iyalai
Gaba da komai, Sabuwar Shekarar Sinawa dama ce ta sake saduwa da iyali. Mutane suna tafiya daga kusa da nesa don haduwa tare da masoya. Cin abincin dare tare da iyali na shekara-shekara, wanda aka sani da “Nian ye fan”, lokaci ne na musamman don haduwa, cudanya da raba albarkatu na shekara mai zuwa. Iyalai suna cin abinci tare a kan babban teburin cin abinci, suna ba da turare don girmama kakanni, kuma suna musayar hongbao.
Tsaftace Gida da Gyaregyare
A cikin makon dake kafin sabuwar shekara, iyalai sukan shiga yin aiki tsabtace gida sosai, suna nuna alamar kawar da datti da makamashi mara kyau daga gidajensu.
Kayan Ado –
Ja shi ne launi na farko da aka yi amfani da shi a cikin ilimin taurari na kasar Sin, wanda ke nuna sa’a da wadata. Ana yi wa gidaje a kasar Sin ado da jajayen kayan ado, da jan fitilu, da jajayen balan-balan, da jajayen kyandir, da jajayen kafit, da sauran jajayen alamomi masu kyaun gani.
Asalin Tatsuniyar ‘Loong’ ta kasar Sin
“Loong”, wata alma’ara ce mai kama da abin da aka sani a yammacin duniya a matsayin dragon, alama ce ta al’ummar kasar Sin. Kuma shekarar 2024 ita ce shekarar da alamar tauraronta ya zo daidai da dabbar Loong.
Jama’ar kasar Sin suna alfahari da Loong tun zamanin da, sun yi imani cewa dabbar ta na raye, ba ta mutu ba kuma na tafiyar da tsarin ruwa a sama da kasa kuma tana da iko sosai. Sarakuna a zamanin da suna da imanin cewa su zuri’ar dabbar Loong ne, yayin da suke nuna halaccinsu na sarauta kuma suna jaddada karfin ikonsu akan jama’a. Tun daga wannan lokacin, Loong ta zama wata muhimmiyar alama a tarihin kasar Sin.
Zamanin Yangshao
Al’adun Loong na kasar Sin yana da dogon tarihi. Zamanin Yangshao, wani zamani ne da ya wanzu a tsakiyar kasar Sin, wanda ke da tarihin shekaru 5,500 zuwa 7,000, a wancan zamanin aka fara bayyana nau’ikan Loong na asali, irin su ichthyosaurs, dragon din maciji, dragon din alade, dragon din kada. Bayyanar wadannan kayan tarihi na farko masu siffar Loong yana da alaka da kusanci da bautar yanayi.
Ayyukan zamantakewa a wacnan zamani bai bunkasa ba. Addinin jama’a na farko shine gama gari kuma mutane sun gaskata cewa “dukkan abubuwa na da dabi’ar dabba.” Wasu tsire-tsire da dabbobi wadanda ke da alaka da rayuwar wayewa ta farko ko kuma suke da tasiri ga al’ummun wancan lokaci sun zama ababen bautar yanayi.
Zamanin Longshan
Zamanin Longshan, yau shekaru 4,000 zuwa 5,000 da suka gabata, ya kasance wani muhimmin mataki na samuwar wayewar kasar Sin. A cikin wannan lokacin, musayar al’adu ya samu bunkasuwa. Siffofin dabbar Loong na musamman a arewa da kudu sun fara cudanya, kuma a wannan lokaci ne cudanyar salon kada da maciji suka bayyana a matsayin siffar Loong. Wannan sabon siffar Loong din ya kunshi karin ruhi kuma yana da kusanci da Loong na abin bauta.
Sifofin Loong na zamanin Longshan sun kunshi macizai da kadoji, kuma suna da halayen damisa, kifi da sauran dabbobi. A matsayin alamar ikon sarauta, ana ci gaba da inganta hoton Loong.
Al’adar Taosi al’ada ce ta masu binciken yanayin hallita na zamanin Longshan, kuma girman tsarin Loong wani muhimmin siffa ne na al’adun Taosi. Yawancin farantin tukwane da aka tono daga kasa suna nuna sifofi iri daya na Loong dake dauke da kan Loong mai siffa kada da kayan ado mai kama da kaho a kansa.
Daular Xia da Shang
A zamanin daular Xia da Shang, wanda aka yi la’akari da dauloli na farko na kasar Sin da suka fara kimanin shekaru 4,000 da suka wuce, Loong ta kara zama wata alama ta samuwar kasa. Al’ummar Xia kabila ce mai son jama’a da juriya. Dangane da kwayoyin halittar al’adu, ba wai kawai sun yarda cewa Loong kakansu ne kuma abin bauta ba, har ma da cewa Loong yana da alaka ta kut-da-kut da rayuwar kabilarsu.
A shekara ta 2002, an gano wani jirgin ruwa da aka kera da dutsen turquoise mai siffofi daban-daban sama da 2,000 a kauyen Erlitou dake lardin Henan, wanda ya kunshi kai da jikin Loong. Bayan dubban shekaru na juyin juya halin halitta da hadewa, a karshe, dabbar Loong ta zama alama ta ruhaniya da al’adu ta kasar Sin.