Tun da gurbatar iska da kuma amincin makamashi sun zama manyan damuwa a duniya, Motocin Sabbin Makamashi (NEVs) na daya daga cikin hanyoyin magance wadannan matsalolin. Kasar Sin ta dauki matakai game da masana’antar NEV kuma ta yi nasara.
Ta hanyar yin amfani da dabaru uku da suka hada da fasaha, kasuwa da manufofi, idan muka dubi manufofi a matakin kasa daga matakai uku na bunkasuwar NEV dangane karbuwarsu a kasuwa, za mu fahimci dalilai uku na bunkasuwar NEV a kasar Sin kamar haka, na farko, gwamnati da kasuwa ne suka jagoranci tsarin hanyar fasaha ta NEV. Na biyu, yanayin kasuwa na sauyawa, don haka an tsara manufofin da ke dacewa da wadannan motocin sabbin makamashi kan lokaci tare da hangen nesa.
- CMG Ya Shirya Harkar Cudanyar Al’adu A Birnin Budapest Don Murnar Cika Shekaru 75 Da Kulla Huldar Diplomasiyya Tsakanin Sin Da Hungary
- Shugaba Xi: Har Kullum Sin Da Hungary Na Kallon Alakarsu Daga Mahanga Mai Fadi Da Wa’adi Mai Tsawo
Na uku kuma, gwamnati ta yi kwaskwarima da kuma daidaita matsayinta game da motoci masu aiki da sabbin makamashi a kan lokaci.
Daga taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da aka gudanar a watan Nuwamban 2017, za mu iya ganin cewa, gurbacewar iska ya zama abin damuwa da manyan kasashe ke fama da shi saboda mummunan tasirin da yake yi ga rayuwar jama’a. Alkaluma daga Tsarin Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi sun nuna cewa, bangaren sufuri ne ke da alhakin samar da kusan kashi 23% na jimillar hayakin carbon mai dumama yanayi wato CO₂. Sabili da haka, akwai yarjejeniya game da bukatar rage hayakin CO₂ da bangaren sufuri ke samarwa ta hanyar taimakon motoci masu aiki da sababbin makamashi (NEVs). Idan aka kwatanta da motocin gargajiya, NEVs suna da fa’ida wajen kiyaye makamashi da kariyar muhalli. NEVs suna ba da dama ga aikin sufuri mara gurbata muhalli, da magance matsalolin zamantakewa da muhalli ta hanyar rage gurbataccen iska don inganta muhalli. An ba da shawarar habaka NEVs a matsayin daya daga cikin hanyoyin da suka fi dacewa don magance matsalar makamashi da gurbacewar muhalli. La’akari da wannan ne kasar Sin ta shige gaba wajen tabbatar da ayyukan kiyaye muhalli ta hanyar rage iskar carbon my dumama yanayi yayin da ta dauki kaso mafi girma a kasuwar motocin sabbin makamashi na duniya.
Tsimin makamashi wani muhimmin al’amari ne da ya yi sanadiyar shaharar NEVs a kasar Sin, kuma daya daga cikin manyan abubuwan da kasar ta sa a gaba. Sakamakon haka, kasar Sin ta karfafa gwiwar masana’antar ta NEV, kuma ta samu ci gaba cikin sauri daga bangarorin fasaha da kasuwanni, alal misali, kasar Sin tana a matsayin koli dangane da samar da fasahar batir yayin da ta zama kasuwa mafi girma ga NEVs. Masana’antar NEV za ta ci gaba da girma cikin sauri a cikin shekaru masu zuwa kuma NEVs za su mamaye kasuwar motocin kasar Sin nan da shekarar 2050.
Cinikin Motocin Sabbin Makamashi A Kasar Sin Ya Zarce Miliyan 30 a shekarar 2023
A shekara ta 2023, cinikin motocin sabbin makamashi a kasuwannin kasar Sin ya karu da kashi 12.0% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata zuwa guda miliyan 30.094 wanda ya wuce miliyan 30 a karon farko. A cewar kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin (CAAM), hasashen da aka yi na shekarar 2024 ya kai guda miliyan 31. Cinikin BYD ya karu sosai daga motoci guda miliyan 1.869 zuwa guda miliyan 3.024, wanda ya tashi daga matsayi na 6 zuwa na 3. A daya hannun kuma, kamfanin Dongfeng, wanda ya kasance a matsayi na 3 ya sauka zuwa matsayi na shida. A kasuwar motocin fasinja, kamfanonin kera motoci na kasar Sin sun kai kashi 56.8% na kasuwar da guda miliyan 14.799, wanda ya nuna karuwar da kashi 23.7% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Kamfanonin NEV Na Kasar Sin Za Su Ninka Cinikinsu A shekarar 2024
A shekarar 2023, yawan motocin da aka kera ya zarce guda miliyan 30.16, wanda ya karu da kashi 11.6 cikin dari a duk shekara, kuma yawan motocin da aka sayar ya zarce guda miliyan 30.09, wanda ya karu da kashi 12 bisa dari, a cewar kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin, adadin da ya kafa tarihi, a cewar CAAM.
Sakatare-janar na kungiyar motocin fasinja ta kasar Sin, ya shaidawa jaridar Global Times cewa, fitar da NEV zuwa kasashen waje zai zama “babban al’amari” a masana’antar motocin kasar Sin nan da shekaru 10 masu zuwa. “Tun da mun ketare ma’aunin samarwa da sayarwa na motoci miliyan 30, wanda ya kai kashi 33 cikin 100 na kasuwannin duniya, dole ne mu tsara wani buri na gaba don kara yawan samarwa da sayarwa na wadannan motocin fiye da miliyan 40 ko miliyan 50,” “Hakan yana nufin za mu rike fiye da kashi 40 zuwa kashi 50 na kasuwan motocin a duniya,” a cewar sa.
Kasar Sin Ta karfafa Tsarin Masana’antar NEV Don Tallafawa Ci Gaba Mai Inganci
Kasar Sin ta kara zayyana sabbin masana’antunta na motocin makamashin lantarki (NEV) don saukaka bunkasuwar fannin mai inganci da kuma karfafa karfin ci gaban da yake samu.
A baya-bayan nan dai, hukumar raya kasa da kawo sauyi ta kasa da wasu hukumomi uku sun fitar da wani tsari na dunkule yadda ake hada NEVs cikin tsarin samar da wutar lantarki a kasar. Nan da shekarar 2025, za a kafa tsarin ma’aunin fasaha na farko na kasar Sin na wannan dunkulewar, kuma za a aiwatar da tsarin farashin wutar lantarki da ake amfani da shi na lokacin cajin NEV da kuma inganta shi. Nan da shekarar 2030, NEVs za su kasance wani muhimmin sashe na tsarin tsimin makamashin lantarki na kasar, bisa ka’ida. Kasar Sin ta fitar da jerin tsare-tsare da ka’idoji na masana’antar NEV, inda ta bayyana hanyoyin ci gaban fannin da nufin gaggauta sauya kasar zuwa cibiyar samarwa da kera motocin. A watan Nuwamba na shekarar 2020, kasar Sin ta gabatar da wani shiri na raya masana’antu daga shekarar 2021-2035, inda ta lissafta ayyuka biyar bisa manyan tsare-tsare, da suka hada da inganta karfin kirkire-kirkire da fasahohin kasar, da gina sabbin nau’o’in muhallin masana’antu, da sa kaimi ga hadin gwiwar masana’antu da bunkasuwa, da kammala tsarin samar da ababen more rayuwa na kasar, da zurfafa tunani da bude kofa da hadin kai.
A watan Afrilun shekarar da ta gabata, ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi taro domin nazarin halin da ake ciki na tattalin arzikin kasa da ayyukan tattalin arziki, kuma taron ya jaddada muhimmancin karfafawa da fadada fa’idojin ci gaban NEV. A cikin watan Yuni 2023, aikin jagoranci don bunkasa da inganta ayyukan samar da cajin NEV ya jaddada bukatar kokarin gina ingantaccen tsarin caji a cikin birane, da mai da hankali kan daukar nauyin caji a wuraren zama da kasuwanni. Haka kuma za a gina ingantaccen tsarin cajin batir yankunan karkara, bisa ga ka’idar, kuma za a gina wuraren gwaji a gundumomi da biranen don aiwatar da ayyukan caji. Kasar Sin ta kuma yi kokarin fitar da damar yin amfani da NEV ta cikin gida ga kasashen waje a cikin shekarar da ta gabata. a Yunin 2023, a wani babban yunkuri, ta tsawaita manufofin harajin sayayya na fifiko ga NEVs zuwa karshen 2027. Kananan hukumomi sun kuma aiwatar da takamaiman matakan karfafawa a karshen shekarar da ta gabata don bunkasa sayayya. Alal misali, birnin Suzhou da ke lardin Jiangsu na gabashin kasar Sin, ya bullo da manufar bayar da tallafin yuan na dijital ga masu sayen motocin. Kamfanonin kera NEV na kasar Sin sun kammala shekarar 2023 da kyakykyawan aiki fiye da yadda ake tsammani, inda aka kiyasta siyar da motocin fasinja masu aiki da sabbin makamashi ya haura kashi 38 cikin dari, a cewar bayanan da kungiyar motocin fasinja ta kasar Sin ta fitar.
Daga cikin masu kera NEV da dama da suka samu karuwar ciniki, kamfanin BYD na Shenzhen ya zama kan gaba a duniya wajen sayar da zallar motocin lantarki a cikin rubu’i na hudu na shekarar 2023. Kamfanin ya sanar da sayar da motoci masu amfani da wutar lantarki guda 526,409 tsakanin Oktoba da Disamba, wanda ya zarce na Tesla. Tare da goyon bayan manufofi masu karfi da kuma karin bukatun cikin gida da ke karuwa, fannin ya samun kyakkyawan mafari a wannan shekara. Wadanda ke cikin masana’antar suna hasashen ci gaba mai karfi, suna tsammanin samarwa da sayarwa na NEVs na kasar Sin za su kara habaka.
Yawan NEV na kasar Sin da aka fitar karu da kashi 27.1% a watan Janairun 2024
Fitar da motocin sabbin makamashi na kasar Sin (NEVs) ya ci gaba da ingantuwa, inda aka fitar da sabbin motocin fasinja 95,000 zuwa kasashen waje a watan Janairun shekarar 2024, wanda ya karu da kashi 27.1 cikin dari a shekara, bisa ga bayanan da kungiyar motocin fasinja ta kasar Sin ta fitar. NEVs da aka fitar sun kai kashi 26.8 cikin 100 na jimillar motocin fasinja da aka fitar a cikin watan, kamar yadda bayanai suka nuna. A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ce, “Girman fa’idar masana’antar motocin sabbin makamashin kasar Sin tare da karuwar bukatar kasuwa, na nufin karin sabbin kayayyakin makamashin da kasar Sin ta kera na samun karbuwa a kasashen ketare.” A sa’i daya kuma, an samu karin karbuwa yayi da masu kera motocin na kasar Sin ke ci gaba da inganta hanyoyi ba da hidimomi masu nasaba da hajarsu a kasashen ketare, wadanda dukkansu ke inganta fitar da NEV ta kasar Sin zuwa ketare. Dangane da bayanan yawan ciniki kuma, kananan motocin samfurin A0 masu inganci sun kai kusan kashi 60 cikin 100 na cinikin NEV da kasar Sin ta ke fitarwa a kasuwannin ketare, kungiyar ta kara da cewa kamfanin SAIC na Shanghai ya ba da rahoton kyakkyawan ci gaba a Turai yayin da BYD ya zama zakarar kasuwar kudu maso gabashin Asiya a farkon shekarar 2024.