A yanzu haka ana gudanar da taron dandalin tattauna batutuwan kimiyya da fasaha na Zhongguancun na shekarar 2023 a nan birnin Beijing. A wani taron dandali makamancin haka da aka gudanar a ranar 26 ga wata, shugaban gidauniyar hadin gwiwa ta Bill da Melinda Gates, Bill Gates, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce, kasar Sin na taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar kalubale masu sarkakiya a duniya.
Bill Gates ya ce, a yayin da ake tinkarar matsalar samar da abinci a duniya, kasar Sin ta gabatar da shawarar hadin gwiwar samar da abinci ta kasa da kasa, wadda ta dauki wani muhimmin mataki kan hanyar sa kaimi ga al’ummar duniya wajen tinkarar matsalar karancin abinci.
Bill Gates ya kara bayyana cewa, a halin yanzu, gidauniyar Gates tana hadin gwiwa da kwalejin nazarin kimiyyar aikin gona ta kasar Sin, domin taimakawa kasashen Afirka su inganta tsarinsu na noman shinkafa bisa tushen kirkire kirkiren fasahohin aikin gona da kasar Sin ke yi. Misali a cewarsa, aikin ya samar da nau’ikan shinkafa da dama da suka dace da yanayin Najeriya da Mali. Kuma wadannan sabbin nau’ikan shinkafa sun taimakawa manoma wajen warware matsaloli da yawa, suna bukatar karancin taki da ruwa, suna iya kara yawan amfanin gona da kashi 50%, sannan za su amfana wajen yaki da bala’un kwari da fari. (Mai fassara: Bilkisu Xin)