Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta zabi shugabanta a karo na bakwai daga mazabar Moriki daga Karamar Hukumar Zurmi ta Arewa.
Sai kuma mataimakinsa Honarabul Adamu Aliyu daga mazabar Gumi ta biyu.
Akawun Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Shehu Saidu Anka ya jagoranci zaben shi5gabanin majalisar.
Kuma nan take Akawun Majalisar Dokokin ya rantsar da Shugabanin Majailisar kamar yadda doka ta tanada.
Haka kazalika, m shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Honarabul Bilyaminu Ismail ya rantsar da sauran shugabannin kwamitocin zauren majalisar don fara aikinta a yau Talata nan take.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp