Wani bincike kan kamfanoni sama da 600 na kasashen waje da hukumar bunkasa harkokin cinikayya ta kasa da kasa ta gudanar, ya nuna cewa, wadannan kamfanoni na kara kwarin gwiwa kan kasuwar kasar Sin.
Fiye da kashi 70 cikin 100 na kamfanonin da aka gudanar da binciken a kansu suna da kyakkyawar fata game da kara bunkasuwar kasuwar kasar Sin a cikin shekaru biyar masu zuwa, wanda ya karu da kusan maki kashi 3.8 cikin 100 idan aka kwatanta da rubu’in da ya gabata.
- Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron OIC Karo Na 15
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Samar Da Damammakin Raya Kai Ga Matasan Kasashen Afirka
Fiye da rabin kamfanonin da aka yi binciken a kansu sun yi imanin cewa, kasuwar kasar Sin ta samu karin armashi, wanda ya karu da maki kashi 2.9 cikin 100 bisa adadin da aka samu a rubu’in da ya gabata.
Bugu da kari, fiye da rabin kamfanonin suna tsammanin zuba jari a kasar Sin zai samar da karin riba a cikin shekaru biyar masu zuwa. A cikin wadannan kamfanoni, kashi 60 cikin 100 sun fito ne daga Turai. (Mai fassara : Yahaya)