Shekaru 70 bayan da kasar Sin ta gabatar da ka’idojin nan 5 na raya zaman lumana, wato martaba ‘yanci da ikon mulkin kasa, da kauracewa nunawa juna karfin tuwo, da kaucewa shiga harkokin cikin gidan juna, da tabbatar da daidaito da cimma moriya tare, da wanzar da zaman lafiya tsakanin sassa daban daban, har yanzu wadannan ka’idoji na ta samun karbuwa, a wannan gaba da huldar kasa da kasa ke fuskantar tangal-tangal.
Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta fitar, ya nuna kaso 82 bisa dari na masu bayyana ra’ayinsu, sun jinjinawa gudummawar Sin bisa kokarinta na wanzar da zaman lafiya a duniya. Kaza lika, kaso 83.5 bisa dari sun bayyana matukar gamsuwa da tasirin ‘yanci, da adalci, da dimokaradiyya dake kunshe cikin wadannan ka’idoji 5 na zaman lumana da Sin ta gabatar, suna masu imanin cewa, Sin za ta ci gaba da tallafawa wajen gina duniya mai kyakkyawar makoma ga sassan kasa da kasa.
Alkaluman jin ra’ayin jama’ar dai sun samu ne daga dandali 2, wadanda CGTN ta samar, wadanda suka samu ra’ayoyin mutane 11,706 daga kasashe 36, ciki har da manyan kasashe irinsu Amurka, da Birtaniya, da Jamus, da Japan, da kuma kasashe masu tasowa irinsu Pakistan, da Indiya, da Afirka ta Kudu, da Brazil da kuma Mexico. (Saminu Alhassan)