“Idan ba ka kan teburin cin abinci, to kai ne abincin.” Amurka, wacce ta yi imani da dokar maji karfi maci gari, tana jan kasashe a yankin Asiya da tekun Pasifik cikin “takardar sunayen abinci”.
Wani binciken jin ra’ayin jama’a da CGTN ya gudanar ta yanar gizo a baya-bayan nan ya nuna cewa, kashi 93.1 cikin kashi 100 na wadanda suka amsa tambayoyin CGTN sun yi imanin cewa, ya kamata a samu tsaro a yankin Asiya da tekun Pasifik ta hanyar tattaunawar siyasa da yin shawarwarin zaman lafiya tsakanin kasashen yankin, kuma suna adawa da yunkurin Amurka na kafa NATO irin na Asiya, wanda ke cike da sigar musamman ta yakin cacar baka da tsokana.
CGTN ya gudanar da binciken ne cikin harsunan Turanci da Faransanci da Larabci da Rashanci da kuma harshen Spain, inda mutane 10,688 suka jefa kuri’a a yanar gizo tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Yahaya)