Batun “Barazanar dorewar kasa”, wani irin furuci ne, wanda Japan take amfani da shi don nuna karfin babakere domin kaddamar da yaki na zalunci ga kasashen waje. A kwanan nan, sabuwar firaministar Japan ta kan yawan ambaton hakan, wanda ya haifar da mummuan tasiri na ra’ayin nuna karfin soja na Japan, inda lamarin ya mamaye fagen ra’ayoyin jama’a na duniya cikin sauri.
Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da kafar yada labarai ta CGTN ta yi a tsakanin masu amfani da yanar gizo a duk duniya ya nuna cewa, jama’ar duniya galibi ne sun yi imanin cewa kalamai da ayyukan firaministar Japan masu muni, alama ce ta sake farfado da ra’ayin nuna karfin soja na Japan, wanda ke bukatar kulawa sosai.
A cikin ‘yan shekarun nan, manufofin diflomassiya na Japan sun sauya cikin hanzari a zuwa “hanyar nuna karfin babakere”, kamar kara kasafin kudin tsaro na shekara bayan shekara, da sassauta takunkumi kan fitar da makamai, da kuma neman habaka makaman yaki. A cikin binciken, kaso 90% na masu bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa Japan tana cikin hadarin maimaita kurakuren ra’ayin nuna karfin soja, kuma sun nuna damuwa sosai game da hakan, kaso 83% na mutanen kuma sun soki gwamnatin Japan saboda ta dade tana karkata daga matsayinta na “kasar zaman lafiya.”
An gudanar da wannan binciken ne a kan dandalin CGTN na harsunan Turanci, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci, kuma cikin awa 24, masu amfani da yanar gizo 7147 ne suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu.(Safiyah Ma)














