A wannan lokacin na hunturu, Harbin na kasar Sin mai lakabin “Birnin Kankara”, ya sake zama wuri mai jan hankali sakamakon gasar wasannin lokacin hunturu ta yankin Asiya da za a yi karo na 9.
Wani bincike da kafar watsa labarai ta CGTN ta gudanar a tsakanin masu amfani da shafukan intanet na duniya, ya nuna cewa, wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu suna fatan ganin an samu karin bude kofa da bunkasa a kasar, suna masu amannar cewa, tattalin arzikin kankara da na dusarta na zama wani sabon nau’in ci gaba ga tattalin arzikin kasar Sin.
- Xi Jinping Zai Halarci Bikin Kaddamar Da Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Lokacin Hunturu Ta Kasashen Asiya Karo Na 9 A Harbin
- Bikin Bazara Na 2025: Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Fara Da Kafar Dama
Gasar wasannin lokacin hunturu ta Harbin ta shekarar 2025 ta Asiya wani babban biki ne na kankara da dusarta na kasa da kasa wadda kasar Sin ta karbi bakuncin shiryawa, bayan gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, kuma ita ce za ta zama mafi samun yawan kasashe da yankuna da ‘yan wasa masu halarta a tarihin gasar wasannin lokacin hunturu na Asiya.
A cikin binciken, kashi 96 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, gasar wasannin ta lokacin hunturu ta Asiya za ta karfafa sha’awar wasannin kankara da dusarta a tsakanin jama’a a kasashen Asiya har ma da daukacin duniya.
Kashi 87.8 bisa dari kuma na masu bayyana ra’ayoyin sun yi amannar cewa, gasar wasannin lokacin hunturun ta Asiya za ta taimaka wajen inganta mu’amala da hadin gwiwa a tsakanin kasashen Asiya, sai kuma kashi 94.7 cikin dari na mutanen da suka bayyana ra’ayoyin sun nuna cewa, bisa ci gaba da inganta manufofin shigowa kasar Sin ba tare da biza ba, suna fatan ganin kasar ta kara bude kofa ga kasashen waje. (Abdulrazaq Yahuza Jere)