Sabuwar gwamnatin Amurka, ta yi amfani da kwanakinta na farko a kan karaga wajen zartar da jerin umarnin shugaban kasa, inda ta sanar da ficewar Amurka daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, da hukumar lafiya ta duniya WHO, wanda hakan ya haifar da damuwa tsakanin sassan kasa da kasa.
Wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ya nuna cewa, manufar nan ta “Sanya Amurka gaban komai”, ba za ta kai kasar zuwa ga sabon “Lokacin cimma Nasarori” ba, kuma hakan zai iya kara haifar da koma baya ga tsarin gudanar da duniya.
- Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Inganta Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa A Taron Davos
- Kwangilar Tashar Wutar Mambila: Obasanjo Zai Bayar Da Shaida A Kotun Paris Yau
Alkaluman sun nuna cewa, kaso 68.5 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na ganin janyewar da sabuwar gwamnatin Amurka ta sanar daga yarjejeniyar Paris, da ficewa daga hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, zai gurgunta hadin gwiwar kasa da kasa, a fannin shawo kan sauyin yanayi, da harkokin kula da lafiyar al’umma. Kaza lika, kaso 77.7 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun yi matukar damuwa, cewa akwai yiwuwar matakin ya haifar da wani mummunan misali tsakanin kasashen duniya.
Alal hakika, har kullum Amurka na kallon hukumomin kasa da kasa, da cibiyoyi, da tsare-tsaren gudanar da harkokin duniya ta wata mahanga maras dacewa, da kuma idon kare moriyar kashin kai, tana kallon su a matsayin wasu abubuwa na cimma nasara, da tabbatar da manufarta ta danniya a duniya.
Karkashin manufar “Sanya Amurka gaban komai”, sabuwar gwamnatin kasar na kokarin matsawa hukumomin kasa da kasa lamba, ta yadda dole za su yi biyayya ga Amurka kan batutuwa irin su kafa dokoki, da yadda za a gudanar da cibiyoyi da jagorancin sauye-sauye, ta hanyar janyewa daga yarjeniyoyin kasa da kasa, da ma wasu hukumomin na kasa da kasa.
Bugu da kari, binciken na jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa, kaso 81.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu, na ganin Amurka na kokarin cimma burikan kashin kai ne, ko da kuwa sauran sassan kasa da kasa za su yi hasara, wanda hakan zai yi matukar illata tsarin gaskiya da adalci a fannin jagorancin harkokin duniya, da halastattun moriyar sauran kasashen duniya.
An dora damar bayyana ra’ayoyin ne kan dandalolin kafar CGTN na Turanci, da Faransanci, da Larabci da yaren Sifaniya da na Rasha, inda masu bayyana ra’ayi sama da 7,452 suka kada kuri’unsu cikin sa’o’i 24. (Saminu Alhassan)