Wani binciken jin ra’ayin jama’a na cibiyar bunkasa ciniki ta Amurka a kudancin Sin, wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na jaridar South China Morning Post dake yankin musamman na HK, ya nuna burin kamfanonin ketare na kara zuba jari a kasar Sin.
Jaridar ta bayyana cewa, karin kamfanonin ketare dake hada-hadarsu a kasar Sin, ciki har da na Amurka, na da burin fadada harkokin kasuwancinsu a Sin cikin shekaru masu zuwa, tare da kara zuba jari don samun riba.
- Rufe Makarantu A Ramadan Ya Tauye Ƴancin Ɗalibai – CAN
- ILO Ta Horar Da Masu Ruwa Da Tsaki Kan Magance Bautar Da Yara a Harƙar Haƙo Ma’adinai
Cibiyar bunkasa cinikayya ta Amurka a kudancin Sin ta gudanar da binciken jin ra’ayi tsakanin kamfanoni 316 dake kudancin kasar Sin, tun daga ranar 11 ga watan Oktoba zuwa 23 ga watan Disambar bara. Kamfanonin da suka kunshi kaso 34 bisa dari na Amurka, da kaso 25 bisa dari na babban yankin Sin, da kuma kaso 14 bisa dari na kamfanonin Turai.
Sakamakon binciken jin ra’ayin ya nuna yadda kamfanonin suka nuna shirinsu na zuba kudi har dala biliyan 14.59 daga ribar da suka samu a kasar Sin, a sabon jarin da za su sake zubawa cikin shekaru 3 zuwa 5 masu zuwa domin fadada kasuwanci da hannayen jarin kasuwar kasar Sin.
Wannan sakamako ya nuna karuwar kaso 33.18 bisa dari, kan wanda aka samu yayin binciken jin ra’ayin da ya gabata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp