Yayin taron ganawa da ‘yan jarida na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, a wani bangare na manyan taruka biyu dake gudana, ministan harkokin wajen kasar, kuma mamba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS Wang Yi, ya bayyana cewa, “Sin da sauran sassan duniya na kara dinkewa waje guda, suna kuma cimma manyan nasarori tare!”
Yayin binciken jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, don gane da “Karbuwar kasar Sin” a idanun duniya, shekaru biyu a jere, kaso 89 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi sun jinjinawa diflomasiyyar kasar Sin, suna masu kallon kasar a matsayin wadda ta cimma tarin nasarori, adadin da ya nuna karuwar kaso 4.8 bisa dari na maki a fannin.
Sakamakon kuri’un jin ra’ayin na CGTN, wanda aka yi tsakanin mutane 32,266 na kasashen duniya 44, ya nuna karbuwar manufofi, da matakai da Sin ke aiwatarwa, a matsayinta na babbar kasa mai bin salon diflomasiyya mai halayyar musamman na Sin. Masu bayyana ra’ayoyin na da burin ganin Sin ta taka karin rawar gani a harkokin jagorancin duniya, da fannin gina salon cudanya na adalci da daidaito.
Kafar CGTN, da jami’ar Renmin ta kasar Sin, karkashin cibiyar tattauna harkokin kasa da kasa a sabon zamani ta Sin ne suka gudanar da binciken.
(Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp