Matakan harajin fito na Amurka na haifar da koma-bayan tsarin cinikayyar duniya. Game da wannan batu, kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ta gudanar da wani binciken jin ra’ayin al’umma ga masu amfani da intanet na sassan kasa da kasa, inda suka yi tir da irin wannan abun da Amurka ta yi, al’amarin da a cewarsu, ka iya janyo ramuwar gayya daga kasashe daban-daban, har ma zai iya ta’azzara yakin harajin fito a duniya, da kawo babbar illa ga tattalin arzikin duniya.
Kashi 82.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna cewa, yayin da ake fuskantar rashin daidaiton ci gaba da karfin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, neman cike gibin cinikayya da Amurka ta yi, abu ne na matukar rashin hankali. Akasarin kasashen da Amurka take neman kara musu harajin kwastam, kasahe ne dake tasowa. Don haka, kashi 82.96 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun yi Allah wadai da abun da Amurka ta yi, na kai wa sauran kasashe harin da babu bambanci kan harajin kwastam, kana a ganinsu, hakan zai iya tauye wa kasashe daban-daban hakkin neman ci gaba, musamman kasashe masu tasowa. Sai kuma kaso 79.58 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu na ganin cewa, sanya harajin ramuwar gayya ya riga ya zama sabuwar hanyar da kasar Amurka take bi wajen aiwatar da tsarin kariyar cinikayya, al’amarin da zai tsananta yanayin cinikayyar duniya, da kawo baraka ga tattalin arzikin kasa da kasa.
An gabatar da wannan binciken jin ra’ayin al’umma cikin harsuna daban-daban na CGTN, ciki har da Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci, da kuma Rashanci, inda masu amfani da intanet 9600 suka bayyana ra’ayoyinsu a cikin awoyi 24. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp