Taron koli na kungiyar G20 na bana, mai taken “Gina duniya mai adalci da wanzar da duniyar bil adama”, na fatan magance yanayin tangal-tangal, da yanayin sauye-sauyen harkokin kasa da kasa, da tarin kalubale masu sarkakiya a fannin jagorancin duniya.
Yayin da ake wannan yunkuri, sakamakon wani binciken jin ra’ayin jama’a na kafar CGTN ta kasar Sin, ya nuna yadda masu bayyana ra’ayoyi suka gamsu da kyakkyawar gudummawar Sin, a fannin ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, da bunkasa jagorancin duniya a fannin.
Binciken ya nuna cewa, kaso 92.8% na masu bayyana ra’ayi sun aminta da muhimmiyar gudummawar Sin a fannin bunkasa wakilci, da daga muryoyin kasashe masu tasowa, da masu saurin ci gaba, a fannin jagorancin harkokin kasa da kasa. Kazalika kaso 91.4% sun amince cewa, Sin muhimmin jigo ce a fagen ingiza ci gaba, da farfadowa, da cimma nasarar kafa duniya mai walwalar bai daya, ga daukacin kasashe masu tasowa da masu saurin ci gaba. (Saminu Alhassan)