Dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya janye sabuwar bukatar da ya shigar na tilastawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta bai wa wakilansa damar shiga aikin tantance takardun zabe da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Bayan haka, kwamitin mutane uku na alkalai karkashin jagorancin mai shari’a Joseph Ikyegh, ya yi watsi da sabuwar bukatar ta Dan takarar ya shigar.
A baya dai jam’iyyar PDP da Atiku sun samu umarnin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a kotun daukaka kara da ke Abuja domin duba kayayyakin da aka yi amfani da su wajen zaben da ya samar da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin zababben shugaban kasa.
Lauyan jam’iyyar PDP da Atiku, Joe-Kyari Gadzama (SAN), a jiya ya sanar da kotun cewa sun janye sabuwar bukatar biyo bayan ganawar da kwamitin lauyoyin jam’iyyar suka yi da INEC a ranar Talata.