Dandalin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin CIIE karo na takwas, shi ne irinsa na farko da aka yi bayan cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiya na 20 na jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS. Baje kolin ya jawo hankalin kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 155, inda fadin yankunan nune-nunen da adadin kamfanonin da suka halarci dandalin suka kafa sabon tarihi. Wani binciken ra’ayin jama’a da CGTN na babban rukunin gidajen rediyo da talibiji na kasar Sin wato CMG ya gudanar da ya shafi mutane 14,000 a cikin kasashe 46 na duniya ya nuna cewa, kashi 72.6% daga cikinsu na ganin cewa, kasuwar Sin ta kasance mai budaddiyar kofa dake cike da karfin takara cikin ‘yanci. Mutane daga kasashe 28, adadin da ya dauki kashi 60 na jimilar kasashen da aka gudanar da binciken, sun amince sosai da wannan batu.
Dagewa kan samun ci gaba tsakanin bangarori daban-daban, wani muhimmin abu ne da ya fito fili a CIIE. A karon farko, an kafa “shagon na musamman na kayayyakin kasashe mafi karancin ci gaba”, wannan shagon ba kawai ya fadada kayayyakin Afirka ba, har ma ya samar da shagunan nune-nune kyauta da kuma fa’idodin haraji na sayar da kayayyaki, hakan ya ba wadannan kayayyaki damar shiga kasuwar Sin kai tsaye. A cikin binciken, kashi 88.2% na ganin cewa, babbar kasuwar Sin wata babbar dama ce ta ci gaba ga kasashe masu tasowa.
CGTN da jami’ar Renmin ta Sin ne suka hada hannu wajen gabatar da wannan bincike, ta hanyar cibiyar nazarin watsa labarai ta kasa da kasa ta zamani. An gudanar da wannan bincike kan jama’ar manyan kasashe mafi ci gaba da kasashe masu tasowa.(Amina Xu)














