Babu wata hujja da ke nuna cewa Shugaban Rasha Bladimir Putin na da tabin hankali ko kuma yana fama da lalurar kwakwalwa, a cewar Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Amurka CIA.
An yi ta samun jita-jita a baya-bayan nan cewa Mista Putin, wanda ke cika shekara 70 da haihuwa a 2022, na fama da rashin lafiya kamar cutar daji, wato kansa.
Sai dai William Burns ya ce babu wata hujja da ke tabbatar da hakan, yana mai cewa “da alama ma lafiya ta yi masa yawa”.
Ita ma Fadar Kremlin ta Rasha ta yi watsi da ikirarin rashin lafiyar shugaban a matsayin “labarin boge”.
Lamarin na zuwa ne yayin da Amurka ke cewa za ta aika wa Ukraine karin makamai masu dogon zango.
Tun farko Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Labrob ya ce yanzu muradin Rasha ba wai “kwace gabashin Ukraine ba ne kawai”, yana mai cewa manufarta ta sauya sakamakon ba wa Ukraine irin wadannan makamai.
‘Mutumin da ya yi imani da karfin iko’
“Akwai jita-jita mai yawa game da lafiyar Shugaba Putin kuma mu dai abin da muka sani shi ne yana cike da koshin lafiya,” a cewar Mista Burns yayin wani taro na tsaro mai taken Aspen Security Forum a Colorado.
Da yake mayar da martani cikin raha, ya kara da cewa kalaman nasa ba su ne karshe ba game da rahoton hukumomin leken asiri.
A ranar Alhamis ta makon jiya ne Fadar Kremlin ta musanta batun rashin lafiyar ta Mista Putin bayan wasu da suka kira kansu “kwararru kan tattara bayanai” sun yada labarai daban-daban kan lafiyar shugaban.
“Amma ba wani abu ba ne illa labarin karya,” kamar yadda kakakin Putin, Dmitry Peskob, ya fada wa manema labarai.
Mista Burns wanda ya yi aiki a matsayin jakadan Amurka a Moscow, ya ce ya sha yin hulda da shugaban na Rasha fiye da shekara 20.
Mista Putin “ya tasirantu da karfin iko, da tilasta wa mutane, da ramuwar gayya” kuma wadannan halaye sun kara tsauri cikin shekara 10 da suka wuce yayin da adadin mashawartansa ke kara raguwa, a cewar shugaban na CIA.
“Ya yi imanin cewa kaddara ce ta shardanta masa a matsayinsa na shugaban Rasha ya mayar da kasar kan turbar iko. Yana ganin babbar hanyar yin hakan ita ce ya fadada iko a makwabtansa kuma ba zai iya yin hakan ba har sai ya samu iko kan Ukraine.”
Mista Burns ya je Moscow a watan Nuwamba don yin gargadi ga Rasha idan ta sake ta afka wa Ukraine bayan sun samu rahotannin shirin yin hakan.
Sai dai Shugaban na CIA ya ce ya bar kasar “cikin damuwa fiye da sanda ya shige ta”.
Ya kara da cewa: “Putin ya yi imani sosai da manufarsa.
Na sha jin sa yana fada a boye tsawon shekaru cewa Ukraine ba cikakkiyar kasa ba ce.
“To, cikakkun kasashe na iya mayar da martani kuma abin da Ukraine ke yi ke nan.”
Amurka ta yi hasashen cewa an kashe dakarun Rasha kusan 15,000 a Ukraine kuma an raunata wasu kusan 45,000, in ji Mista Burns.