Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta sanar da Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti.
Mista Oyebanji ya yi nasara a kananan hukumomi 15 cikin 16 da ke jihar.
- Yau Ake Gudanar Da Zaben Gwamna A Jihar Ekiti
- ‘Yan Siyasa Sun Yi Ruwan Naira A Ekiti Wurin Saye Masu Kada Kuri’a Da Jami’an Tsaro
APC ta samu kuri’u 178,057, SDP ta samu 82, 211, sai PDP wadda ta samu 67,457.
Zaben wanda a lokacin da ake tsaka da gudanar da shi an samu bullar wasu rahotanni da ke cewa ana cinikin kuri’ar masu zabe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp