Firaministan Birtaniya, ya yi kira ga ‘yan kasar mazauna Lebanon su gaggauta ficewa daga kasar a daidai lokacin da fada tsakanin Hezbollah da Isra’ila ke kara kazancewa.
Sir Keir Starmer ya ce “Muna duba shirin da ya kamata mu yi, amma ina ganin ya kamata ku fice daga kasar, saboda akwai hadarin barkewar yaki”.
- Ofishin Jakadancin Sin Dake Najeriya Ya Gudanar Da Liyafar Murnar Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Sabuwar Kasar Sin
- Bani Da Wani Buri A Yanzu Da Ya Wuce In Ganni A Dakin Mijina – Khadija Muhammad
Ma’aikatar tsaron Birtaniya za ta girke dakaru 700 a Cyprus, domin shirin ko ta kwana na kwashe ‘yan kasar daga Lebanon, sannan ta gargadi matafiya su kaucewa zuwa kasar.
Kawo yanzu sojin Isra’ila sun hallaka sama da mutum 500 tun bayan kaddamar da hari a Lebanon ranar Litinin, ciki har da mata da kananan yara 150.