Jama’a da ke biye da mu a wannan shafi na Dausayin Musulunci assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barkatuh. Idan ba a manta b+a, a makonni biyu da suka gabata, muna bayani ne a kan kyawon cika alkawarin Annabi (SAW) amma saboda munasabar Maulidin Hadimin Manzon Allah (SAW), Shehu Ibrahim Inyass sai muka yi karatu game da gudunmawar da bayar a cikin Musulunci, to, duk dai har yau a cikin Manzon Allah ne, tun da Shehu Hadiminsa ne (SAW). Yau za mu yi waiwaye a darasinmu na farko sannan mu kawo karashensa don ya zama karatu bai-daya.
Kamar yadda ya zo a karatun namu na baya, dabi’un Annabi (SAW) na cika alkawari da mutunta abokan zama na baya da sada zumunci, alkali Abu Amiru ya zantar da mu cewa, Abul Hamsha’i ya ce, “na yi ciniki da Annabi (SAW) kafin Allah ya aiko shi a matsayin Annabi, sai sauran kayan suka rage a hannuna babu, zan je in kawo masa ragowar, da na tafi sai na manta, ban tina ba sai da kwana Uku ta yi, sai na zo zan wuce, sai na gan shi a inda na bar shi, sai ya ce min ya kai saurayi, ka wahalar da ni, ina nan inda ka bar ni, kwana Uku ina jiranka.
An karbo daga Anas, Hadimin Manzon Allah (SAW), ya ce, Annabi (SAW) ya kasance idan aka zo masa da kyauta, ya diba wanda zai yi amfani da shi ya rabar da wasu, sai ya ce, a diba wasu kuma a kai gidan kawar Sayyada Khadijah (alkawarin zama da ita) sabida ta kasance tana son Sayyada Khadijah.
Sayyada Khadijah ita ce uwar Musulunci baki daya, da kudinta aka fara kafa Musulunci, bayan rasuwarta sai kudin Sayyadina Abubakar sannan kuma kudin Ganima da ya fara zuwa wa Musulunci. Annabi (SAW) ya rike mata alkawari, ya rike ma Sayyadina Abubakar alkawari, Allah ya rike musu alkawari, ya turo Mala’ika Jibrilu ya gaishe da Sayyada Khadijah ya ce wa Sayyadina Abubakar “Allazi yu’udi malahu yatazakka, wa mali’ahadin indahu min ni’imatin tujza, illabtiga’a wajhi rabbihil a’ala, walasaufa yarda.”
An karbo daga Sayyada A’isha tana cewa “Ni ban yi kishi da wata ‘ya mace ba, sai da wacce ba ta nan tana Lahira (Sayyada Khadijah) sabida yadda ake kula da ita. Da yawa Annabi (SAW) zai yanka dabba amma sai ya aika da naman gidan kawayen Sayyada Khadijah.”
Sayyada A’isha tana cewa, “Mata, ku bar kishi, kishi ya hana mu haihuwa.” Sayyada A’isha ta kasance in Annabi (SAW) yana hirar Sayyada Khadijah cikin Matanshi sai ta dakatar da shi, sai Annabi (SAW) ya kau da kai, hakkinta ne, wata rana sai ta ce masa, “Wai Allah bai sauya maka ba ne, ya tafiyar da bazawara ya ba ka budurwa”, Annabi (SAW) ya ce “wallahi Allah bai canza min ba, wace ce kamarta, kowa ya kafirce min ita ta yi Imani da ni, kowa ya hana ni, ita ta ba ni dukiyarta kuma ita ce uwar ‘ya’yana,” daga nan Matan Annabi (SAW) suka san ba za su haihu ba. Don haka, dukka ‘ya’yan Annabi (SAW) daga dakin Sayyada Khadijah suke, sai daya Ibrahimal Mu’azzam daga baiwa ‘yar Afirka (Mariyatul Kibdiyya).
Wata rana ‘yar`uwar Sayyada Khadijah ta zo wurin Annabi (SAW) tana neman izini, sai aka ga Annabi (SAW) yana farin ciki da murna kamar wani sarki ya zo.
Sayyada A’isha ta ce, “wata rana, wata mata ta zo wurin Annabi (SAW), sai aka gan shi ya sakar mata fuska, yana ta hira da ita yana nishadi, bayan ta koma, sai aka tambaya, wai wace ce wannan? Sai Annabi (SAW) ya ce, kawar Khadijah ce, haka take zuwa mana zamanin Sayyada Khadjah.”
“Tina kyakkyawan Alkawari yana daga cikin Imani,” ku dinga tina ‘yan`uwanku na Allah, kar ku manta da su.
Wani daga cikin Sahabbai yana siffanta Annabi (SAW), sai ya ce “Ya kasance yana sada zumunta”. Annabi (SAW) wata rana ya ce, “Dangin gidan wane, ba sa so na, amma dangina ne, ku kai musu kyautata.”
Wata rana Annabi (SAW) ya yi Sallah wa Sahabbai tare da jikarsa Umamatu, ‘yar Sayyada Zainabu tana dauke a kan kafadarsa, in ya yi Sajjada sai ya sauke ta, in ya mike ya dauke ta, Abul’asi shi ne mahaifinta, mutum ne mai alkawari ya yi wa Annabi (SAW) Alkawari kuma ya cika.
Abul’asi yana daga cikin wadanda aka kama a yakin Badr, kowa yana biyan fansa a sake shi, sai Matarsa Zainabu ‘yar Manzon Allah (SAW) ta turo da sarkar mahaifiyarta (Sayyada Khadijah) mai tsada a matsayin kudin fansa, da Annabi (SAW) ya ga sarkar Sayyada Khadijah, ya ce wannan Sarkar Khadijah ce ba ta Abul’asi ba, sai suka yi alkawari da Annabi (SAW) cewa, zai maida wa Zainabu Sarkarta shi kuma zai je ya nemo kudin fansarsa sannan zai turo Zainabu zuwa ga mahaifinta, ya kuma cika alkawari ya turo ta shi kuma ya tafi kasuwancin nemo kudin fansarsa.
Wata rana ya fita kasuwanci, a hanya ya hadu da tawagar Musulmai suka kwace dukkan kayan kasuwancinsa har da na Mutanen Makkah da yafito da su. In ya koma Makkah, bai da kudin biya sai ya gudo wurin Matarshi (Zainabu) cikin dare a Madina, da Asubah Annabi (SAW) ya shiga Sallah sai Zainabu ta zo Masallaci wurin Annabi (SAW) ta ce Abul’asi dan Rabi’a ya zo wurina a dare a matsayin bakona kuma yana cikin kiyayewata, sai Annabi (SAW) ya gaya wa Sahabbansa abin da ‘yarsa Zainabu ta ce. Annabi (SAW) ya sa aka maida masa da kayansa da aka kwace, ya koma Makkah ya maida musu da kayansu sannan ya dawo Madina ya Musulnta.
An karba daga Abi Katadata ya ce, tawagar ‘yan aike daga Sarki Najjashi sun zo wa Annabi (SAW), sai Annabi (SAW) ya tashi da kansa yana yi musu Hidima, sai Sahabbai suka ce Ya Rasulallahi, ka zauna za mu yi maka, sai ya ce musu “Mutanen Najjashi ne, sun girmama mutanenmu da suka yi Hijira zuwa Habasha, ina so in saka musu.”
Yayin da aka zo da ‘yar uwarsa ta shayarwa da ake kira Shaima’u a cikin ribatattun yakin Hunaini, ta bayyana wa Annabi kanta da cewa ita ce Shaima’u, `yar`uwarsa wurin shayarwa, sai Annabi (SAW) ya shimfida mata mayafinshi, ya ce mata, in tana so tazauna tare da shi, ta zama `yar`uwa abar girmamawa, in kuma tana so ya ba ta kyauta mai yawa ta koma wurin mutanenta, sai ta zabi mutanenta, Annabi (SAW) ya ba ta kyauta mai yawa.
Sahabi Abuddufaili ya ruwaito cewa, yana yaro, ya ga Annabi (SAW) wata rana wata Mace ta matsanto kusa da shi har ya cire mayafinsa ya shimfida mata sai ta zauna a kai, ni kuma sai na tambaya wai wacece wannan ne? sai aka ce Uwa ce wacce ta shayar da shi Nono (Halimatus Sa’adiyya).
An karba daga Amru dan Sa’ibi yana cewa, wata rana Annabi (SAW) ya kasance yana zaune sai Babansa na shayarwa – Mijin Halimatus Sa’adiyya ya zo wurinsa, sai Annabi (SAW) ya shimfida masa rabin bargonsa ya zauna a kai sannan ya shimfida ma Babarsa ta shayarwa – Halimatus sa’adiyya dayan rabin bargon, sannan kuma dan uwansa ya zo na shayarwa, sai ya tashi tsaye ya zaunar da shi a kusa da shi sabida girmamawa. Annabi (SAW) ya kasance yana aike wa Suwaibatul Aslamiyya da kyauta a-kai-a-kai, yayin da ta rasu, sai ya tambaya, waye ya ragu a cikin makusantanta, sai aka ce ya rasulallahi duk su rasu.
Suwaibatul Aslamiyya, Baiwar Abu Lahabi ce, wacce ta yi wa Abu Lahabi busharar cewa matar dan`uwansa ta haihu, sabida farin ciki ya ‘yanta ta kuma ita ta fara shayar da Annabi (SAW) kafin Halimatus Sa’adiyya, sabida wannan aikin da ya yi, duk ranar Litinin ana ‘yanta shi daga wutar Jahannama.
A cikin Hadisin Sayyada Khadijah, yayin da Annabi (SAW) ya dawo daga kogon Hira yana ce mata ta lullube shi yana tsoron Aljanu sun bude masa Ido, sai ta ce, ka yi bushara, Ubangijinka ba zai tozarta ka ba sabida kana sada zumunta, kana daukar nauyin wanda ba shi da shi, kana garar baki, kana taimakon mutane a kan jarrabawar da Allah ya yi musu. Me yin wannan kuma, Allah ba zai tozarta shi ba.
Alhamdu lillah, wannan fasali na rike alkawarin zama (Husnul ahdi) ya kammala. Fasali na gaba zai tsakuro wasu daga cikin ‘Kankai da kai na Annabi (SAW)’.