Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, kuma babban jami’i a sashen binciken tsattsauran ra’ayi a cibiyar ‘Tony Blair for Global Change’, Bulama Bukarti, a ranar Lahadi, ya yi gargadin cewa ayyukan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, sun fara samun mabiya a manyan kafafen sada zumunta irin su TikTok.
Bukarti ya bayyana haka ne yayin da ya kasanace babban bako a shirin Siyasa na Gidan Talabijin na Channels.
- Ibtila’i: Ma’aikatan Ruwa 4 Sun Rasa Ransu A Bauchi
- Har Yanzu Ruhin Taron Bandung Yana Tare Da Mu Wajen Kara Karya Lagon Babakere
Wannan fallasa na zuwa ne mako guda bayan Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya koka kan yadda jihar Borno ta yi asarar sojoji 100 da fararen hula 280 a hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai cikin watanni shida.
Sai dai Bukarti wanda ya shafe shekaru da dama yana gudanar da bincike kan kungiyar ta ‘yan ta’adda, ya kara nuna fargabar cewa, a halin yanzu ‘yan tada kayar bayan na yaɗa aƙidarsu a shafukan sada zumunta ta hanyar ɗora naɗaɗɗen faifan bidiyo da kuma gabatarwa kai tsaye.
Ya ce, “Yanzu idan ka shiga TikTok, za ka ga shafukan ‘yan Boko Haram, suna gudanar da shirye-shirye kai-tsaye ko kuma su ɗora naɗaɗɗen bidiyo, inda suke yada akidar Boko Haram, suna kafa hujjar kashe-kashen da suke yi da harshen Hausa, suna amsa tambayoyi daga masu sauraro, suna amsa tsokaci da aka rubuta.
“Ko a wannan makon ma, an samu wani dan Boko Haram da ya saka wani bidiyo na mintuna 10 a TikTok yana kai min hari saboda na yi magana kan karuwar ta’addancin kungiyar, amma ba wannan kadai ba, mun san cewa Boko Haram a yanzu suna sarrafa jirage marasa matuka, suna sa ido kan tsarin soja a yankin arewa maso gabas da jirage marasa matuka.
“Abin da muka gani cikin watanni uku da suka wuce shi ne hare-hare bakwai da ‘yan Boko Haram suka kai a manyan ssansanonin a sojojin Nijeriya. A Sabon Gari da sauran wurare da dama sun mamaye sansanonin, sun tarwatsa sojoji, sun kashe wasu, sannan sun kama wasu, suka sace makamai, abinci, magunguna da sauran kayan aiki daga yankunan, suka gudu cikin daji.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp